Katsina Times
Ƙungiyar tsoffin mambobin jam’iyyar ANPP da ke cikin APC ta nemi a bar wa bangarensu kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027, tana mai gargaɗi cewa za su sake nazarin matsayin su a jam’iyyar idan ba a yi adalci ba.
A wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja, ƙungiyar ta bayyana cewa tun bayan haɗewar jam’iyyu da aka kafa APC a 2013, bangarensu na ANPP yana fama da wariya da rashin damawa da su a siyasa. Sun bayyana cewa sun taka rawar gani wajen kafa da samun nasarar APC a zaɓe, amma ba su sami sakamako mai kyau ba.
Shugaban ƙungiyar kuma tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ANPP na ƙasa Farfesa Vitalis Orikeze Ajumbe, ya ce, “Zaben da kake yi a kai yanzu zai samu cikas idan ka zaɓi wanda ba daga bangaren ANPP ba a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.”
Ya kuma ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna halin ko-in-kula da su, duk da cewa ANPP na da manyan ‘yan siyasa da suka haɗa da mataimakin shugaban ƙasa yanzu, Sanata Kashim Shettima, gwamnonin jihohi da dama da kuma tsofaffin gwamnoni da sanata da ‘yan majalisu.
Ƙungiyar ta nuna damuwa cewa har yanzu ba su da isassun mukamai a gwamnatin Tinubu, kuma sun nemi a tabbatar da adalci da raba madafun iko bisa yadda aka kulla yarjejeniyar haɗakar jam’iyyun da ta haifi APC.
Sun jaddada cewa a yayin da CPC ta mulki ƙasa na tsawon shekara 8 karkashin Buhari, yanzu ACN ke rike da shugabancin ƙasa, don haka lokaci ya yi da za a rika damawa da ANPP ta hanyar ba ta damar samar da mataimakin shugaban ƙasa da kuma shugabancin ƙasa a 2031.