Jihar Katsina Za Ta Karɓi Bakuncin Bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na Farko

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12082025_155722_FB_IMG_1755014160077.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 12 ga Agusta, 2025

Hukumar Tarihi da Al’adu ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta kammala shiri domin gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya a karo na farko da goyon bayan gwamnati, wanda zai gudana a ranar 26 ga Agusta, 2025, a Daura, tare da halartar ƙasashe akalla 24.

Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Dandalin tunawa da Dr. Mamman Shata da ke kan titin Jibiya, ranar talata 12 ga watan Agusta, Daraktan Hukumar, Dr. Kabir Ali Masanawa, ya ce wannan shekara za ta kasance ta musamman wajen nuna tarihin Hausa, al’adu, fasaha, gadon tarihi da kuma abincin gargajiya ga duniya baki ɗaya.

“Mun yi cikakken shiri. Jiya mun ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Daura domin neman albarka da kuma ƙarfafa tunawa da tarihinmu na Hausawa,” in ji Dr. Masanawa. “Gadonmu, abincinmu da karamcinmu abin alfahari ne. Jihar Katsina tana cikin kwanciyar hankali, kuma muna gayyatar duniya ta zo ta shaida wannan biki.”

Ya ƙara da cewa Gwamna Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya umurci hukumar ta yi aiki tare da ƙungiyar shirya Ranar Hausa ta Duniya domin tabbatar da biki na girmamawa.

Shima a jawabinsa, Abdulbaqi Aliyu Jari, ɗan jarida na ƙasa da ƙasa mai aiki da TRT a birnin Istanbul, kuma ɗaya daga cikin masu jagorantar shirye-shiryen Ranar Hausa, ya bayyana cewa an fara bikin Ranar Hausa a 2015 domin girmama harshen Hausa da al’adunsa. Ranar 26 ga Agusta na tunawa ne da gyare-gyaren rubutun Hausa da masanin Jamus, Hans Fischer, ya yi a shekarun 1920s.

“Yanzu Hausa na matsayi na 11 cikin manyan harsuna a duniya, kuma ana hasashen zuwa 2050 za ta zama na biyar,” in ji Jari. “Wannan biki yana ɗaga harshenmu da al’adunmu zuwa sahun manyan al’adu na duniya. A bana za a gudanar da bikin a ƙasashe 24, ciki har da Netherlands a karon farko.”

Za a gudanar da babban bikin a fadar Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar, CON, wanda ya kasance mai kishin al’adu da tarihin Hausawa. Masu shirya taron sun bayyana cewa za a samu wasannin gargajiya, nunin kayan tarihi, da nune-nunen karamcin Hausawa, tare da watsa shirye-shirye kai tsaye ga masu kallo a duniya.

Follow Us