Jam’iyyar NNPP ta lashe zaɓen cike gurbi na mazabar Bagwai/Shanono a majalisar dokokin jihar Kano.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen, Hassan Adamu Shitu ne ya bayyana haka a yau Lahadi.
Shitu ya ce dan takarar NNPP, Ali Hassan Kiyawa, ya samu ƙuri’u 16,198, inda ya doke na APC, Ahmad Muhammad Kadamu, wanda ya samu ƙuri’u 5,347.
Wakilin da ya rasu a mazabar, Halilu Ibrahim Kundila, ɗan jam’iyyar APC ne, kuma ya rasu a watan Afrilu 2024.
Da wannan nasara, NNPP ta ci gaba da zama jam’iyya mai rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano da mambobi 26, yayin da APC ke da mambobi 14.
A ranar Asabar, APC ta nemi hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta soke zaɓukan jihar.
Mai magana da yawun APC na ƙasa, Felix Morka, ya bayyana cewa an “cika zaɓen da tarzoma mai tsanani da kuma tada jijiyoyin wuya daga ‘yan daba masu makamai a wurare daban-daban.”
Ya ce rahotanni daga Shanono, Bagwai da Ghari sun nuna cewa masu zaɓe sun tsere daga rumfunan ƙuri’a yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin shawo kan lamarin.
Kuma kwamishinan INEC a Kano, Audu Zango, ya tabbatar da cewa an kama sama da mutum 100 da ake zargin ‘yan daba ne yayin zaɓen cike gurbin na Bagwai.
Mai magana da yawun NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, ya soki kiran na APC na a soke zaɓen, inda ya bayyana shi a matsayin “ba shi da tushe kuma ba shi da gaskiya.”
Johnson ya jaddada cewa zaɓen ya gudana cikin gaskiya, adalci da lumana, tare da nuni da cewa kasancewar Kano gadon NNPP ne, abin da ba zai yiwu ba shi ne sakamakon ya karkata a wata jam’iyya.