Gwamnatin Tarayya Ta Fara Rijistar Shirin Horas da Matasa 100,000 a Fannin Ilimin Hada-Hadar Kuɗi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21082025_200202_president-tinubu-1440x710.jpg


Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara rijistar matasa domin shiga cikin shirin koyar da ilimin Hada-Hadar kuɗi kyauta da zai horas da matasa 100,000 a kowace shekara a fannin kasuwancin duniya, ƙirƙirar sana’o’i da zuba jari. Daraktar Sashen Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Cigaban Matasa, Omolara Esan ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja, inda ta ce an haɗa gwiwa da Investonaire Academy wajen aiwatar da shirin.

Ta bayyana cewa shirin zai taimaka wajen ba matasa dabarun fahimtar manyan fannonin kasuwanci na duniya kamar harkar kayan masarufi, zinare, hannayen jari da musayar kuɗaɗen kasa da kasa (forex). Haka kuma, za a koyar da su dabarun magance hatsarin afkawa hasara a kasuwanci, yadda za a samar da kundin jarin kasuwanci da hanyoyin haɓaka tattalin arziƙi. Ta ce duk wanda ya kammala za a ba shi takardar shaidar da masana’antu ke amincewa da ita wacce za ta taimaka wajen cigaban haɓakar kasuwanci.

Esan ta ƙara da cewa horon zai gudana ta hanyar tsarin Learning Management System (LMS) da ke haɗa darussa cikin salo na zamani. Haka kuma, za a fara horon kai tsaye a Abuja nan gaba kadan kafin a miƙa shi zuwa sauran jihohi. Ta jaddada cewa shirin kyauta ne, kuma a buɗe yake ga dukkan matasan Najeriya ciki har da ɗalibai, masu bautar ƙasa (NYSC), ‘yan kasuwa, masu neman aiki da ƙwararrun matasa a faɗin ƙasar.

Follow Us