Shugaban kamfanin MSM Group, Alhaji Mu’azzam Mairawani, ya bayyana cewa shirye-shiryen jawo hannayen jari na gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samar da sama da dala biliyan 15 a masana’antar man fetur da gas.
Mairawani ya ce goyon bayan da Shugaban Ƙasa ya basu ya ƙarfafa musu guiwa wajen faɗaɗa harkokinsu da kuma jawo sabbin hannayen jari daga waje, inda aka samu sama da Dala biliyan 15.
Ya ƙara da cewa kamfanin na MSM, ta hannun rassan da ya mallaka, na gab da kammala yarjejeniyar a Amurka da darajarta ta kai dala miliyan 225, wadda ake sa ran za a kammala cikin wannan watan.
Mairawani ya ce burinsu shi ne su kawo jarin dala biliyan 2.7 kowace shekara a Najeriya, tare da ƙara faɗaɗa dama a fannoni daban-daban da suka haɗa da mai da gas, siminti, jiragen ruwa da kuma makamashi.
Mairawani ya yi godiya ga Shugaban Ƙasa, al’ummar Najeriya da abokan hulɗa na ƙasashen waje bisa goyon bayan da suka nuna. Ya kuma bayyana cewa kamfanin MSM zai ci gaba da bayar da gudummawa wajen samar da ayyukan yi, raya ƙasa da kuma inganta rayuwar jama’a.