Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Rahotanni daga jaridun ƙasashen waje da Katsina Times ta tattaro sun tabbatar da cewa Mayor na birnin Istanbul, Ekrem Imamoğlu, na fuskantar tuhuma a kotu bisa zargin amfani da digirin bogi. Wannan batu na iya zama barazana ga burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a Turkiyya.
Imamoğlu, wanda ke da farin jini a tsakanin jama’a, ana kuma ɗaukar shi a matsayin ɗan siyasar adawa mafi ƙarfi da zai iya kalubalantar Shugaba Recep Tayyip Erdoğan a zaɓen 2028, ya ce waɗannan zarge-zargen ba komai ba ne illa shirin hana shi yin takara.
Binciken ya samo asali ne tun daga lokacin da Jami’ar Istanbul ta soke digirin da ta bayar wa Imamoğlu, bisa hujjar cewa canjin digirinsa daga wata jami’a a Cyprus ba ya da ingantaccen daidaiton ƙasa.
Rahotannin Hurriyet Daily News da Daily Sabah da Katsina Times ta duba sun nuna cewa lauyoyin gwamnati sun gabatar da ƙarar a kotu, inda ake neman a yanke masa hukunci tsakanin shekaru 2.5 zuwa 8.75 a gidan yari.
A Turkiyya, dokar ƙasa ta tanadi cewa duk wanda zai tsaya takarar shugaban ƙasa dole ne ya mallaki digiri daga jami’a. Wannan na nufin cewa soke digirin Imamoğlu na iya zama barazana kai tsaye ga cancantarsa.
An kama Imamoğlu ne a ranar 19 ga Maris, 2025, bisa wasu zarge-zargen rashawa da almundahana, sannan aka tsare shi yayin da ake cigaba da shari’a. Wannan mataki ya tayar da tarzoma a Istanbul da sauran manyan biranen Turkiyya, inda dubban magoya bayansa suka fito kan tituna suna kira da a saki shi.
Jaridar The Guardian ta bayyana wannan zanga-zangar a matsayin mafi girma da aka gani a Turkiyya cikin shekaru goma.
Imamoğlu ya dade yana fuskantar matsin lamba daga gwamnati. A shekarar 2022, wata kotu ta same shi da laifin “zagin jami’an gwamnati” tare da yanke masa hukuncin shekaru biyu da rabi a gidan yari da kuma dakatar da shi daga siyasa. Duk da yake ba a aiwatar da wannan hukuncin ba saboda har yanzu yana shari’a a matakin ƙara, lamarin ya nuna irin kalubalen shari’a da siyasa da ya sha a baya.
Imamoğlu ya musanta dukkanin zarge-zargen, yana mai cewa gwamnati na amfani da kotu da dokokin jami’a wajen hana shi damar yin takara.
A wata sanarwa da lauyoyinsa suka fitar, sun ce: “Wannan shari’a ba ta da tushe. Ana son a tauye ‘yancin ɗan adam da tsarin dimokuradiyya a Turkiyya.”
Martani daga ƙasashen ketare:
Kungiyoyin kare hakkin ɗan adam da suka haɗa da Human Rights Watch sun soki tsarewar, suna cewa wannan wani ɓangare ne na matsin siyasa da gwamnatin Erdoğan ke yi kan ‘yan adawa.
Rahoton Reuters ya nuna cewa abokan hulɗa na Turkiyya a Turai suna kallon wannan lamari a matsayin wata barazana ga tsarin dimokuradiyyar ƙasar.
Shari’ar digirin bogi da ake yi wa Ekrem Imamoğlu ta buɗe sabon babi a siyasar Turkiyya, inda ake ganin zata iya shafar tsarin zaɓe na gaba. Duk da cewa ba a yanke masa hukunci ba tukuna, rahotanni daga jaridun ƙasashen waje da Katsina Times ta tattaro sun nuna cewa wannan lamari na iya zama ɗaya daga cikin manyan gwaje-gwajen dimokuradiyyar ƙasar a nan gaba.