2025: Shekarar kaddamar da Manyan littattafai da tone-tone a littafan da aka wallafa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28122025_221208_FB_IMG_1766959832395.jpg



Daga Danjuma Katsina

Shekarar 2025 ta zo da wani sabon salo na adabi fiye da kowace shekara a tarihin Najeriya. Yayin da ake kallon bayyana rubutu a yanar gizo ya ]an dankwafe rubutu a littafi, 2025 sai ta zo da amsar cewa, ko ba da]e ko ba jima za a koma ma bun}asar rubutu a littafin, su tafi kafa]a da kafa]a da rubutun yanar gizo.

Shekarar 2025 sai ta zo da wani salon tone-tone da bayyana sirri a cikin rubutun littafin, sai ya zama mutane suna ~oye wani lamari har sai a littafin da suka rubuta za a gan shi. Ba a ta~a shekarar da aka fitar da sabbin littatafai suka bayyana da yawa ba, kamar wannan shekarar ta 2025.

Na bi nazarin shekaru goma da suka wuce, na }ara tabbatar da yawan littattfan da aka gabatar a shekarar 2025 sun fi na kowace shekara a cikin shekaru goman da suka gabata, kana kuma iya cewa sune gaba a tarihin Najeriya. 

Jadawalin littattafan suna da yawan gaske, kamar yadda na tara su. Amma zan kawo ka]an, sunayen su da marubutan, wanda kowa zai iya sanin cece-kucen da suka kawo ko kuma ilmin da aka saki a cikin su.

A shekarar ne tsohon Shugaban }asa Janar Ibrahim Babangida ya fitar da littafinsa mai suna: A Journey In Service: An Autobiography of General Ibrahim Babangida. A kuma shekarar ne Malam Ibraheem Yaqoub El-zakzaky shi ma ya fitar da nasa 'autobiography' ]in mai suna Rayuwata.

A shekarar Malam Garba Shehu ya bayyana aikin sa da Atiku da zaman sa da Buhari a fadar Shugaban }asa da littafin sa mai suna "According to the President: Lesson from Presidential Spokesman's Experience.  

A shekarar ne }ungiyar mawallafan jaridu a yanar Gizo mai suna GOOCOP suka wallafa littafin yadda suka kafa kungiyar da tarihin aikin jarida a yanar gizo a duniya da Najeriya mai suna: GOOCOP Perspectives on Online Publishing. 


Ri}a}}en attajirin nan Femi Otedola, shi ma ya fitar da littafin darasin rayuwar shi a harkar kasuwanci da littafin sa mai suna: The Making It Big.

Jaridar da ta fi tsufa a arewacin Najeriya, wadda ake bugawa da Hausa mai suna Almizan, ita ma ta yi bukin cika shekaru 35 ana buga ta da }addamar da littafin tarihin kafuwar ta mai suna: Tarihin Almizan Da Gwagwarmayar ta.

A shekarar ne tsohon Ministan watsa labaran Najeriya, wanda ya fi }aurin suna a tarihin Najeriya, ya gabatar da nasa littafin mai suna: Headline And Soundbites: Media Moment That Define An Administration.

Wani littafin da ya ta da }ura shi ne mai suna: From Soldier To Statesman: The Legacy Of Muhammadu Buhari, wanda Charles Omole phd ya rubuta, Shugaban }asa da iyalan marigayi Shugaban }asa suka }addamar da shi. Amma abin da ke ciki, kamar cin fuska ne ga mamacin, Muhammadu Buhari. 

Iyalan hamsha}in Attajirin nan, ba a bar su a baya ba. Watau zuriyar Alhassan [antata da ke Kano sun fitar da littattafai biyu a shekarar masu suna: Behind The City Wall da kuma Aminu Dantata: Life And Times of Nigeria Entrepreneur, wanda Munzali [antata ya rubuta. 

Wani littafin da ya fito shi ne mai suna: Beyond Airwaves of a commentator, encounter and experience by Dayo Alabi.

Tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido ya girgiza }asa da littafinsa mai suna: Being True To Myself. Ya yi tone-tonen da har yanzu ana maganar su.

Tsohon mai magana da yawun Shugaban }asa a zamanin mulkin Jonathan, Reuben Abati, ya yi bukin cika shekarar sa sittin a duniya da }addamar da littatafai guda uku. Taron, wanda ya samu halartar manyan mutane a fa]in Najeriya. 

Malam Ibrahim Sheme, marubucin littafin Shata Ikon Allah, ya fitar da littafinsa mai suna Tarihi Da Wa}o}in Uwani Zakirai a shekarar 

Mai shari'a Ado Bello, shi ma ya fitar da littafinsa mai suna: Eyes Of The Law a shekarar. 

A karon farko aka fitar da littafin mai ya faru ga wasu mutane da suka yi gudun hijira don kar su zauna }ar}ashin mulkin Turawa? Marubucin ya yi takakkiya daga Najeriya har }asar Sudan don binciken, ya fitar da littafinsa mai suna: Sokoto Caliphate In Diaspora Na Shu'aibu Bello.

Wani littafin da ya ]au hankali shi ne mai suna Zaria Massacre na Ibrahim Musa, wanda ya tattauna da ganau da wadanda suka tsira a rikicin 'yan Shi'a da sojoji, wanda ya faru a Zaria a shekarar 2015.

Writing For Media And Monetising It, wanda Vice Chairman na Leadership Media Group ya rubuta, Azu Ishiekwene; littafin shi ma ya ci kasuwa sosai. 

Masoya gwamnatin Tinubu su ma sun fitar da nasu littafin mai suna: Reflections of President Bola Ahmed Tinubu: Renewed Hope Agenda.

Binciken da kuma na yi a Hukumar Tetfund, mun gano a shekarar 2025, Tetfund ta taimaka wajen buga littatafai masu yawa na malaman jami'o'i da kwalejoji fiye da kowace shekarar a shekarun baya.

A karon farko na samu littattafai, wa]anda aka buga da harsunan gida wa]anda suka shafi ilmin fasaha da kimiyya a wannan shekarar, misali littafin Ilmin Crypto A Sau}a}e da Hausa na Abdullahi Mahuta. Sai Zamba a Internet, shi ma da Hausa.
A jahar katsina an fitar da wani littafi da ya kumshi sunaye da tarihin mutane dari da suka bada gudummuwa ga gina Najeriya. 
Zuri ar Dallazawa sun fita da wani littafin da ya kumshi gudummuwar da mulkin su ya bada a cigaban jahar katsina. 
Wani littafin da gidauniyar sardaunan katsina Ahmad Rufai ta fitar ya bayyana yadda sarakuna kan iya  taka rawa a matsalar tsaron kaasar nan.

A shekarun baya, ba a samu irin wannan ambaliyar fitar littattafai ba kamar bana,
Wasu littattafai da suka yi tone-tone a shekarun baya akwai One Step Ahead, A Life As A Spy And Detective By Former EFCC Boss Farida Waziri. 

Akwai Stepping On Toes, My Odyssey at the Nigerian Ports Authority by Hadiza Bala Usman.

Akwai Aristocratic Rebel, The Biography of MD Yusuf By Ayo Opadukun.

2025 ta tabbatar da cewa, duniyar rubuta littafi ba ta mutu ba, amma ta ]an yi barci ne,  kuma ta fara farfa]owa. Wannan alama ce ta cewa a gaba, duniyar karatu a littafi na iya dawowa da }arfin ta.
Danjuma katsina  Mawallafi ne kuma dan jarida dake tare da kamfanin katsina times media group 
08035904408.08020570059

Follow Us