An Rantsar Da Sabbin Shuwagabannin Kungiyar "Arewa Consultative Forum" Ta Kasa Reshin Jihar Katsina.

KATSINA TIMES.A ranar Alhamis 19 ga watan Yuni na shekarar 2025, aka rantsar da sabbin shuwagabannin kungiyar "Arewa Consultative Forum"....

Katsina City News June 19, 2025  ·  12:00 AM
| 1,405 Views


KATSINA TIMES.

A ranar Alhamis 19 ga watan Yuni na shekarar 2025, aka rantsar da sabbin shuwagabannin kungiyar "Arewa Consultative Forum" ta kasa rashin jihar Katsina. Rantsuwar ta samu jagorancin Barista A.A Ahmad 

An rantsar da sabbin shuwagabannin kungiyar ne biyo bayan gabatar da zabe da akayi a ranar 12 ga watan Mayu na wannan shekara da muke ciki, wanda daga karshe Shehu Musa Malumfashi ya zama sabon shugaban kungiyar, a matakin jiha.

A nashi jawabin jim kadan bayan shan rantsuwa. Shehu Musa Malumfashi ya bayyana kudurin shi na yin aiki tukuru a matsayin shi na sabon shugaban kungiyar ya kuma shaida cewa nan da dan lokaci kadan sabbin tsare tsare zasu bayyana wadanda zasu cigabantar da kungiyar gaba.

Shehu Musa Malumfashi ya kara da cewa akwai abubuwa da yawa wadanda suke damun yankin arewa to yana da kyau al'umma su bada hadin kai wajen ganin tabbatar da dorewar zaman lafiya da kuma cigaban yankin, dama kasa baki daya.

Ya kara da cewa zasu hada kai da gwamnoni da duk wanda suka san bai bada gudunmawa ta kowace bangare domin cigabantar da kungiyar, ya kuma nemi hadin kan sauran ya'yan kungiyar to samar da sabon sauyi a kungiyar.

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 4?