Shugaban Dikko Project Movement Ya Sabunta Rajistar Katin APC a Katsina

Shugaban Dikko Project Movement Ya Sabunta Rajistar Katin APC a Katsina Shugaban kungiyar Dikko Project Movement, Hon. Musa Gafai, ya....

Katsina City News January 22, 2026  ·  12:00 AM
| 1,057 Views

Shugaban Dikko Project Movement Ya Sabunta Rajistar Katin APC a Katsina


Shugaban kungiyar Dikko Project Movement, Hon. Musa Gafai, ya sabunta rajistar katinsa na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a mazaɓarsa ta Yamma II da ke Ƙaramar Hukumar Katsina, Jihar Katsina.

An bayyana cewa Hon. Gafai ya ɗauki matakin ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinsa na ƙarfafa jam’iyyar APC da kuma nuna cikakken goyon bayansa ga burin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, na sake neman nasara a zaɓen 2027.

Advertisement

Da yake jawabi bayan sabunta rajistar, Hon. Musa Gafai ya ce sabunta katin jam’iyya na da matuƙar muhimmanci wajen bai wa mambobi damar taka rawar gani a harkokin zaɓe da kuma goyon bayan shugabanni nagari masu kishin al’umma. Ya jaddada cewa rajistar katin jam’iyya na ƙarfafa dimokuraɗiyya tare da tabbatar da sahihanci da tsari a tafiyar siyasa.

Ya ƙara da cewa haɗin kai, biyayya da bin ka’idojin jam’iyya su ne muhimman ginshiƙai da ke tabbatar da nasara da dorewar dimokuraɗiyya, tare da bunƙasa jam’iyya mai ƙarfi da ingantaccen shugabanci.

A ƙarshe, Hon. Gafai ya yi kira ga magoya bayansa da mambobin APC, musamman na mazaɓar Yamma II, da su fito su sabunta rajistar katinsu domin ƙara tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 8 + 7?