Da babu TETFund, da manyan makarantun Najeriya sun ruguje – Farfesa Adamu Abubakar Rasheed

Daga Wakilanmu @ Katsina TimesTsohon Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Adamu Abubakar Rasheed, ya bayyana cewa da babu Hukumar Asusun Tallafawa Manyan Makarantu ta Ƙasa (TETFund), da manyan…

Katsina City News October 16, 2026  ·  12:00 AM
| 77 Views
Da babu TETFund, da manyan makarantun Najeriya sun ruguje – Farfesa Adamu Abubakar Rasheed
Da babu TETFund, da manyan makarantun Najeriya sun ruguje – Farfesa Adamu Abubakar Rasheed


Daga Wakilanmu @ Katsina Times

Tsohon Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Adamu Abubakar Rasheed, ya bayyana cewa da babu Hukumar Asusun Tallafawa Manyan Makarantu ta Ƙasa (TETFund), da manyan makarantun gaba da sakandare da jami’o’in Najeriya sun ruguje.

Farfesa Rasheed, wanda ya shafe sama da shekaru 40 yana koyarwa a jami’a, ya bayyana hakan ne a taron Kwamitin Amintattu na Hukumar TETFund da kuma taron tattaunawa da jama’a (Town Hall Meeting) da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.

Taron, wanda aka mayar da hankali kan makomar ilimin jami’o’i da kuma rawar da Hukumar TETFund ke takawa wajen bunƙasa harkar ilimi a ƙasar nan, ya samu halartar masana daga sassa daban-daban, inda aka shafe yini ana tattaunawa kan batutuwan da suka shafi ci gaban ilimi.

A jawabinsa, Farfesa Rasheed ya ce kuɗaɗen da ake warewa manyan makarantun ƙasar nan ba su wadatar wajen biyan buƙatunsu, har ma da kuɗaɗen shiga da suke samu da kansu.

Advertisement

NRS Gateway

Ya bayyana cewa tallafin da Hukumar TETFund ke bayarwa ne ya taimaka wajen farfaɗo da manyan makarantun, tare da ba su damar ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Ya kuma nuna damuwa kan rashin inganta yanayin aiki da walwalar ma’aikatan jami’o’i, yana mai cewa abin takaici ne yadda wasu malamai suka shiga halin ƙuncin rayuwa har kamanninsu ba su bambanta da na mutanen da ke bara ba.

A cewarsa, makomar Najeriya tana cikin gina al’umma mai ilimi, kuma hakan ba zai yiwu ba sai an inganta manyan makarantun ƙasar nan da kuma rayuwar ma’aikatan da ke aiki a cikinsu.

Masari ya ce tallafin TETFund na ƙaruwa

A nasa jawabin yayin buɗe taron, Shugaban Kwamitin Amintattu na Hukumar TETFund, tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, CFR, ya bayyana cewa kuɗaɗen da hukumar ke warewa domin tallafa wa manyan makarantu suna ƙaruwa a kowace shekara tun bayan zuwan gwamnatin da ta hau mulki a shekarar 2023.

Masari ya bayyana cewa ana sa ran kuɗaɗen da za a samu domin tallafa wa manyan makarantu a shekarar 2027 za su iya haura naira tiriliyan ɗaya.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 5?