Wane Laifi Mannir Yakubu, Tsohon Mataimakin Gwamnan Katsina, Ya Yi Wa Jam’iyyar APC?

Nazari da Bincike na MusammanDaga Jaridun Katsina TimesKwanan nan aka ga sunan mai ɗakin tsohon mataimakin gwamnan Katsina, Alhaji Mannir Yakubu, a cikin jerin sunayen shugabannin mata na yaƙin neman…

Katsina City News November 20, 2026  ·  12:00 AM
| 59 Views
Wane Laifi Mannir Yakubu, Tsohon Mataimakin Gwamnan Katsina, Ya Yi Wa Jam’iyyar APC?
Wane Laifi Mannir Yakubu, Tsohon Mataimakin Gwamnan Katsina, Ya Yi Wa Jam’iyyar APC?


Nazari da Bincike na Musamman

Daga Jaridun Katsina Times


Kwanan nan aka ga sunan mai ɗa

kin tsohon mataimakin gwamnan Katsina, Alhaji Mannir Yakubu, a cikin jerin sunayen shugabannin mata na yaƙin neman zaɓen Sanata Yakubu Lado Danmarke, ɗan takarar gwamnan Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Hajia  Mariya Mannir Yakubu... An kuma gan ta a ranar ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen, inda har ta yi hira da manema labarai, ta kuma bayyana cewa tana kira ga al’ummar Katsina da su zaɓi Sanata Yakubu Lado Danmarke.

A cikin shekaru takwas da suka yi suna mulki, Mannir Yakubu da tsohon gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, sun sanya matansu a matsayin uwaye, inda harkokin da suka shafi mata kawai ake ganinsu a ciki. Haka kuma, sun nisanta ’ya’yansu daga duk wani al’amari da ya shafi harkokin gwamnati. An kuma san su da iko a kan iyalansu, ba tare da shiga wani abu da zai jawo wa gwamnati abin magana ba.

A tarihin Katsina, gwamnatin Masari da Mannir Yakubu na daga cikin gwamnatocin da suka zo da kundin rubutaccen tsari na sauya fasalin Katsina zuwa shekaru masu zuwa.

Amma rashin kuɗi da kuma wasu ’yan farar ƙafa da ke cikin gwamnatin sun hana ta samun nasarar aiwatar da abin da ta ƙuduri aniyar yi dari bisa ɗari.

Kafin zaɓen da ya kawo gwamnatin Masari, masana na gaskiya waɗanda suke zaune a Katsina ko kuma yawan zuwa jihar, sun taru a Katsina na tsawon kwanaki suna tattaunawa da fitar da dukkan matsalolin Katsina, tare da hanyoyin da za a bi wajen fuskantarsu.

Rayuwar Aminu Masari da mataimakinsa a lokacin mulkinsu ta zama abin misali a duk faɗin ƙasar nan, har ana rubuta labarinsu a jaridu.

Mannir Yakubu ya nemi takarar gwamna tare da Malam Dikko Radda. Bayan ya faɗi zaɓen fitar da gwani, ya miƙa wuya, ya kuma yi aiki ba dare ba rana domin APC ta samu nasara.

A lokacin, ya haɗa kan ’yan jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Katsina wuri guda. Kowa yana samun haƙƙinsa, kuma kowa yana ba shi girmansa.

Advertisement

NRS Gateway

Bayan kammala gwamnati, ya koma gidansa da ke Layout, wanda ya yi wa kwaskwarima, kuma ya mallaka sama da shekaru ashirin kafin su hau gwamnati.

Ya ci gaba da biyayya ga jam’iyyarsa da gwamnatin APC. Haka kuma, ya ci gaba da kyakkyawar mu’amala da mutanensa, yana ƙarfafa musu gwiwa domin su tabbatar da ba gwamnati goyon baya don ta samu nasara.

Mannir Yakubu ya ci gaba da rayuwarsa tsakanin Katsina, Kaduna da Abuja.

A Ina Aka Samu Matsala?

Mun yi ƙoƙarin magana da tsohon mataimakin gwamnan Katsina, amma abin ya ci tura. Sai dai wani na kusa da shi ya bayyana mana cewa jimloli uku kawai zai yi amfani da su, kuma babu wani ƙari da zai yi.

"Tun da aka kafa gwamnati, ba a bai wa His Excellency darajarsa da martabarsa wadda Allah ne ya ba shi."

Wataƙila, in ji shi, "Don yaƙi zama ɗan fada ne ko kuma ya ƙi zama ɗan tasha. Amma fa gidan da ya fito da tsarin siyasarsa ba zai sa ya  zama ɗaya ba."

Ya ƙara da cewa:

"Mu abin da kawai muke tambaya shi ne, wane laifi Mannir Yakubu ya yi wa jam’iyyar APC?"

Mannir Yakubu tsohon ɗan siyasa ne wanda ya fara siyasa tun yana Jami’ar ABU Zariya, a ƙarƙashin jagorancin Marigayi Yusufu Bala Usman.

Dukkan rayuwarsa ta siyasa ta kasance ne a jam’iyyun adawa, har zuwa shekarar 2015 da suka kafa gwamnati.

Dattijo ne wanda ake girmama dattakunsa. Ya fito ne daga zuriyar malamai da ’yan kasuwa, waɗanda suka shafi Albaba, tsohuwar kasuwa da Gafai.

Shi mutum ne mai karatu, wanda abokansa ke cewa ƙaddara ce kawai ta hana shi zama malamin jami’a.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 8?