Riki A APC: CPC Na Neman Shugabancin Jam’iyyar Na Kasa, ...Sheriff Ya Ce Zabin Mataimakin Shugaban Kasa Na Tinubu Ne

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes01082025_124121_FB_IMG_1754052011154.jpg

Katsina Times 

Wani sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC, inda bangaren CPC ke matsa lamba a ba su shugabancin jam’iyyar na kasa, biyo bayan murabus din Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Kodayake jam’iyyar ta tabbatar da Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaba, CPC ta nuna rashin jin dadinta tare da bukatar a nada tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura.

Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa CPC na jin ana wulakanta su a tsarin mulki na APC tun bayan kafa gwamnatin Tinubu, lamarin da ya kara zafafa rikicin bayan wasu jiga-jigan CPC sun fice daga jam’iyyar, ciki har da Nasir El-Rufai, Abubakar Malami da Babachir Lawal.

Wasu daga cikin mambobin CPC da suka rage a jam’iyyar sun ce suna ci gaba da fuskantar wariya, inda suka bukaci shugabancin APC da ya dauki matakin warware rikicin kafin zaben 2027.

A gefe guda kuwa, Sanata Ali Modu Sheriff ya mayar da martani kan matsin lambar da wasu ke yi don neman kujerar mataimakin shugaban kasa a 2027, inda ya ce wadannan mutane ba wakilan ANPP bane.

“Zabin mataimakin shugaban kasa a 2027 hakkin Tinubu ne. Jam’iyyar APC jam’iyya ce ta kasa, ba jam’iyyar wani yanki ba,” in ji Sheriff a wata hira da Channels TV.

Ya ce duk wanda ke da muradi zai iya tuntubar shugaban kasa kai tsaye, amma babu wanda zai tilasta masa wanda zai dauka a matsayin mataimaki.

Sheriff ya kuma ce rikicin taron APC a Gombe ba shi da nasaba da matsayinsu a jam’iyyar, tare da tabbatar da cewa dole ne a mutunta tsarin da jam’iyya ta gindaya.

“Abin da zai hana Tinubu lashe zabe a 2027 guda biyu ne: ko dai idan babu zabe a Najeriya ko kuma idan ya fasa tsayawa takara,” in ji shi.

Jam’iyyar APC na fuskantar kalubale daga bangarori daban-daban yayin da zaben 2027 ke kara karatowa.

Follow Us