Katsina Times | Alhamis, 1 ga Agusta, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da umarnin dole ga dukkan masu rike da mukaman gwamnati su halarci tarukan jin ra'ayin jama'a da za a gudanar a dukkan gundumomi 361 na jihar, domin tantance bukatun al'umma da kuma samar da kasafin kudin 2026 na 'yan kasa bisa tsarin hadin gwiwa da jama’a.
Wannan mataki ya biyo bayan umarni ne da Mataimakin Gwamna, Mai Girma Faruk Lawal, ya sanyawa hannu a wata takarda, inda aka bayyana cewa tarukan za su fara ne daga Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025 da misalin karfe 10:00 na safe, a wuraren da aka ware a kowace gunduma ko unguwa.
Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ne ya amince da gudanar da wannan tsari, domin baiwa jama’a damar bayyana bukatunsu da kuma inganta tsarin shiryawa da aiwatar da ayyukan ci gaba daga tushe.
Takardar ta bayyana cewa dole ne dukkan masu mukaman siyasa irin su SSAs, TAs, SAs da sauran hadimai na matakin jiha da kananan hukumomi su shiga cikin tarukan, kuma babu wanda aka yafe masa halarta.
Haka kuma, an umarci jami’in gwamnati mafi girma a kowace gunduma da ya jagoranci taron, ya tabbatar da an gudanar da shi cikin tsari, an rubuta bayanai yadda ya kamata, sannan an mika rahoton sakamakon a kan lokaci.
Mataimakin Gwamna ya jaddada bukatar daukar wannan aiki da muhimmanci tare da tabbatar da nasarar gudanar da shi.
Wannan shiri na daga cikin tsarin National Citizens’ Engagement Programme, wanda ke da nufin daidaita tsarin ci gaban jihar da ainihin bukatun jama’ar karkara da birane.