Katsina Times
Ofishin dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Musawa da Matazu, Hon. Abdullahi Aliyu Ahmed, ya mayar da martani ga wata talla da aka biya aka wallafa a shafin jaridar Daily Trust da kuma dandalinta na yanar gizo a ranar Litinin, 23 ga Yuni, 2025, mai dauke da sunan Nuhu Muhammad Aliyu, inda aka zarge shi da yin amfani da takardun boge.
A cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar, Hon. Ahmed ya bayyana cewa zargin da ke cikin tallar ba shi da tushe balle makama, kuma haramtacce ne saboda yana bata masa suna da kimarsa a idon jama’a.
Sanarwar ta ce: “Hon. Ahmed bai taba yin takardun boge ba, kuma ba a taba bincike ko zarginsa da hakan ba daga kowace hukuma. Dukkan takardun da ya gabatar a ayyukan sa na gwamnati da na sirri sahihai ne kuma za a iya tabbatar da su.”
Martanin ya kara da cewa zargin na nuna rashin fahimta da kuma karkatar da gaskiya ne, ya kuma sabawa tsari da doka.
Ofishin ya bayyana Hon. Ahmed a matsayin dan kasa mai bin doka, wanda ke ci gaba da aiki da gaskiya da rikon amana ga al’ummar mazabarsa da Najeriya baki daya.
“Mun bukaci jama’a su yi watsi da zarge-zargen da ke cikin wannan talla da aka biya kudi aka sa, yace an yi ne domin bata masa suna da yaudarar jama'a," inji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ce dan majalisar zai dauki matakin doka don kare sunansa da martabarsa daga irin wadannan kalamai na batanci a nan gaba.
A karshe, ofishin Hon. Ahmed ya jaddada kudurinsa na ci gaba da jagoranci da gaskiya da adalci, tare da godewa daukacin al’ummar Musawa da Matazu da ’yan Najeriya bisa goyon bayan da suke ci gaba da ba shi.
Jaridar Daily Trust ta ranar Talata 29, ga watan Yuli 2025