Shari’ar APC da ’yan takarar: Mun kai ƙara ne don a bi doka – Inji Shugaban APC na jihar Katsina, Dakta Bashir Gambo Saulawa

Muazu Hassan@ Katsina TimesShugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Dakta Bashir Gambo Saulawa, ya bayyana wa jaridun Katsina Times cewa sun kai ƙarar wasu ’yan takarar da suka samu tikitin…

Katsina City News November 12, 2026  ·  12:00 AM
| 85 Views
Shari’ar APC da ’yan takarar: Mun kai ƙara ne don a bi doka – Inji Shugaban APC na jihar Katsina, Dakta Bashir Gambo Saulawa
Shari’ar APC da ’yan takarar: Mun kai ƙara ne don a bi doka – Inji Shugaban APC na jihar Katsina, Dakta Bashir Gambo Saulawa


Muazu Hassan

@ Katsina Times

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Dakta Bashir Gambo Saulawa, ya bayyana wa jaridun Katsina Times cewa sun kai ƙarar wasu ’yan takarar da suka samu tikitin wasu jam’iyyu ne ba don komai ba sai don a bi doka kuma a kiyaye ta.

Bashir Gambo ya ce dokar zaɓe ta bayyana duk yadda za a shiga takara da kuma yadda za a gudanar da zaɓen shekarar 2027.

Dokar ta tsara jadawalin komai, da yadda za a gudanar da shi, da kuma lokacin da za a gabatar da shi. Mun gano cewa waɗannan ’yan takarar sun saɓa wa waɗannan ƙa’idojin zaɓe.

Gambo ya ce: “Dokar nan fa, tana a yanar gizo, kyauta za ka iya sauke ta. Kuma ana samun wadda aka buga.”

Advertisement

NRS Gateway

Gambo ya ce sun bi dokar nan, sun tabbatar a rubuce cewa an saɓa wa ƙa’ida. Saboda haka ne suka tafi kotu domin kotu ta yi musu adalci.

@ Katsina Times

Www.katsinatimes.com

Facebook Page: Katsina City News

Facebook Group: Katsina City News

Facebook Page: Jaridar Taskar Labarai

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 1?