A ranar Alhamis din nan 19 ga Junin 2025 ne, Kungiyar Matasa Ta kasa, wato 'National Youth Congress (NYC)' a turance, bisa jagorancin kwamitin Kaddamarwarta, ta rantsar da sabbin shuganninta na jihar Katsina.
Bikin rantsuwar wanda ya gudana a dakin taro na "Bello Kofar Bai" da ke a Sakatariyar jihar, ya samu halartar dimbin jama'a da suka hada da Wakilan Kungiyoyi al'umma, jami'an gwamnati, shugannin hukumomin tsaro da sauransu.
Da yake gabatar da jawabi a matsayinsa na babban bako a taron, shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar, Honorabul Abdulkadir Mamman Nasir wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, ya hori sabbin shugabannin da su kasance shugabanni nagari, sannan su gudanar da shugabancinsu kan gaskiya da amana.
Bugu da kari, a mamadin gwamnatin jihar, shugaban ma'aikatan, ya yi wa sabbin shugabannin matasan fatan alkhairi da addu'ar jagorancin Allah(S) a cikin aiwatar da shugabancin nasu.
Duk a wajen bikin rantsarwar, Masana harkokin shugabanci, Siyasa da harkokin yau da kullum wadanda suka fito daga jami'o'i daban-daban, sun gabatar da makaloli a wajen don kara haskawa shugabannin dabarun gudanar da jama'a musamman matasa. Daga cikinsu akwai: Dr. Kabir Umar Musa(UMYU), Aliyu Nasir Kankara(KISTIM), Dr. Jamilu M. Abdulsalam, Aminu Yusuf Dikko da sauransu.
A nasa jawabin, sabon shugaban kungiyar, Muhammad Muhammad Mono ya yi alkawalin gudanar da shugancin kungiyar ta matasa a bude, ba tare da nuna bambancin ko kumbiya-kumbiya ba. Hakazalika, ya kuma nemi hadin kan sauran shugabannin da aka zabe su tare yin aiki tukuru domin kai kungiyar koluwar matakin nasara.