Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times Asabar, 21 ga Yuni, 2025
Alhaji Shehu Musa Malumfashi ya karɓi ragamar shugabancin ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) reshen Jihar Katsina, a wani taron miƙa mulki da aka gudanar ranar Asabar, 21 ga Yuni, 2025.
A jawabinsa yayin taron, Alhaji Shehu ya bayyana godiya ga Allah Madaukakin Sarki da kuma mambobin ƙungiyar bisa amincewa da aka yi da shi da sauran shugabanni da aka zaɓa, yana mai alƙawarin shugabanci na gaskiya, adalci da haɗin kai.
“Na karɓi wannan nauyi da tawali’u da kuma niyyar ganin mun cika amana tare da sauran shugabanni da aka zaɓa,” in ji shi.
Ya yaba da kokarin mambobin farko na ƙungiyar, yana jinjina musamman ga Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida, bisa ƙoƙarinsa wajen gina harsashin ACF a jihar. Haka zalika, ya yi wa Wazirin Kankia, Alhaji Lawal Ibrahim Kankia godiya kan jagorantar ƙungiyar a lokacin riko da jajircewa.
“Sun sadaukar da lokaci da kuzarin su domin ganin ƙungiyar ta daidaita kuma ta fara aiki yadda ya kamata a Katsina,” in ji Malumfashi.
Ya tabbatar da cewa sabon shugabancin ba zai nuna bambanci ko wariya ba, yana mai cewa:
“ACF iyali ne. Kowa yana da matsayi da darajarsa. Za mu mutunta kowanne memba tare da bashi hakkinsa.”
Malumfashi ya ce tafiyar shugabancin za ta kasance bisa tsarin shawarar mambobi, ba ra'ayin mutum ɗaya ba. Ya ƙara da cewa abin da zai amfanar da Katsina, Arewacin Najeriya da ƙasar baki ɗaya shi ne ginshiƙin aikinsu.
“Za mu saurari muradun mambobi domin su ne za su ɗora mu kan tafarkin da ya dace.”
Ya yi kira ga dattawa da masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafawa ACF, yana mai yaba da yadda tattaunawa da musayar ra’ayoyi ke gudana a cikin ƙungiyar musamman ta kafar WhatsApp.
“Hangen nesan da mambobi ke nunawa ta hanyar muhawara da ba da ra’ayi na nuna yadda suke da kishin ci gaban ƙungiyar da al’umma.”
Haka kuma, Alhaji Shehu ya nuna shirin ACF na yin aiki tare da Gwamnatin Jihar Katsina, yana mai cewa gwamnatin tana da buɗaɗɗiyar ƙofa ga jama’a da kuma manufofin da suka dace da bukatun talakawa.
“Za mu kasance abokan aiki da gwamnati domin ciyar da Katsina gaba da kawo ci gaba mai ɗorewa.”
A ƙarshe, ya gode wa mambobi bisa goyon bayansu kafin da bayan zaɓe, yana mai alƙawarin cewa sabbin shugabannin za su yi aiki da gaskiya da hadin kai domin cimma manufofin ACF.
Sabbin Shugabanni na ACF, Jihar Katsina:
Alhaji Shehu Musa Malumfashi – Shugaba
Hajiya Wasila Sani Saulawa – Mataimakiyar Shugaba
Alhaji Bello Iro Dabai – Sakataren Ƙungiya
Barr. AbdulKadir B. Isah – Mataimakin Sakataren Ƙungiya
Hajiya Aisha Dauda Daura – Ma’ajiyar Kuɗi
Alhaji Sada Salisu Ruma – Sakataren Yaɗa Labarai
Alhaji Lawal Kasimu Funtua – Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai