Ƙungiyar Abokan Asibitoci Ta Ƙaddamar Da Aikin Agaji A Katsina Saboda Yajin Aikin Malaman Jinya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes31072025_113654_FB_IMG_1753961745424.jpg

Shugaban ƙungiyar ya buƙaci mambobi su shiga aikin agaji a asibitoci

Daga Katsina Times | 31 Yuli, 2025

Ƙungiyar Abokan Asibitoci ta Jihar Katsina ta buƙaci dukkan mambobinta a faɗin ƙananan hukumomi 34 na jihar da su taka rawa wajen bayar da agajin gaggawa da sauran ayyukan jinƙai ga marasa lafiya, sakamakon yajin aikin gargaɗi da Ƙungiyar Nas-Nas da Ma’aikatan Aikin Haihuwa (NANNM) ta ƙasa ta fara a ranar Litinin.

Shugaban ƙungiyar na jihar, Alhaji Bilya Sanda Khadimul Islam, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a Katsina, inda ya jaddada bukatar gaggauta tallafawa cibiyoyin kiwon lafiya don rage wa marasa lafiya radadin yajin aikin.

Alhaji Bilya ya yaba da muhimmancin rawar da nas-nas da ma’aikatan haihuwa ke takawa a fannin kiwon lafiya, yana mai fatan za a warware takaddamar cikin gaggawa da lumana domin amfanin ma’aikatan lafiya da al’umma baki ɗaya.

Ya ce tuni ƙungiyar ta fara karɓar daftarin sa kai daga kungiyoyin agaji kamar haka: Jama’atu Nasril Islam (JNI), Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’iqamatis Sunnah (JIBWIS), Hukumar Red Cross ta ƙasa, Lajnatul Hisbah, da Munazzamatu Fityanul Islam

Wadannan kungiyoyi sun fara gudanar da ayyukan agaji a Asibitin Gwamnati na Katsina da kuma sauran cibiyoyin lafiya a fadin jihar.

Alhaji Bilya ya kuma tabbatar da cewa ƙungiyar ta tanadi abinci, ruwa da sauran kayayyakin buƙata ga duk masu aikin sa kai domin sauƙaƙa musu hidimar jinƙai a wannan lokaci mai ƙalubale.

“Za mu ci gaba da tsayawa tare da marasa lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya a kowane hali,” in ji shi. “Mambobinmu su ci gaba da nuna halin jinƙai, kishin al’umma da haɗin kai wanda su ne ginshiƙan ƙungiyarmu.”

Yajin aikin na nas-nas wanda ke gudana na tsawon kwanaki bakwai ya shafi ayyukan kiwon lafiya a asibitocin gwamnati da dama, lamarin da ya janyo ƙungiyoyi masu zaman kansu shiga don tallafa wa marasa lafiya.

Follow Us