NUJ@70: Yar’adua Ya Yi Kira da a Kiyayi Barazanar Kafofin Sadarwa na Zamani, Ya Yabi Gudunmuwar 'Yan Jarida

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17062025_235228_Screenshot_20250618-005122.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TIMES

Sakataren watsa labarai na Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Malam Abdullahi Aliyu Yar’adua, ya bayyana damuwa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta ta hanyoyin da ke haifar da rudani da barazana ga aikin jarida da amincewar jama’a ga sahihan bayanai.

Yar’adua ya bayyana hakan ne a wajen bikin cika shekaru 70 da kafuwar Kungiyar 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), da aka gudanar a dakin taro na Hayatt Regency Suite da ke Katsina.

Yayin jawabin nasa, Yar’adua ya kawo wani misali cikin nishadi don yabawa Dr. Sama’ila Balarabe, wanda ya gabatar da Lakca a wajen taron. Ya kwatanta halin da ake ciki da gasar rawa tsakanin namun daji, inda kare ya zama alkalin gasar da Kura ke rawa, dole kare ya yaba.

“Koda ban halarci taron ba, ina tabbatar da cewa Dr. Sama’ila ya cancanci yabo,” in ji shi.

Sai dai nan take ya karkata jawabin nasa zuwa ga matsalar da ya kira "barazana mai tsanani" da ke addabar aikin jarida a yau, wato yadda ake amfani da kafafen sada zumunta ba tare da tantance gaskiyar bayanai ba.

“Yanzu kowa na iya daukar wayarsa, ya rubuta duk abin da ya ga dama, ya watsa shi ga duniya. Abin bakin ciki, wasu masu bin su a dandalin sada zumunta na daukarsu a matsayin masu gaskiya,” in ji Yar’adua. “A da kafin a wallafa wani labari, sai an bi matakai na tantancewa da gyara. Amma yanzu an shafe hakan baki daya.”

Yar’adua ya bukaci shugabancin NUJ, musamman a matakin kasa, da su dauki matakin hana yada bayanan karya a kafafen sada zumunta da kuma kare mutuncin aikin jarida da ke da tarihi shekaru 70.

“Hukumomin tsaro ma suna da rawar da za su taka wajen dakile wadanda ke yada bayanan karya don haddasa rikici,” in ji shi.

Yayin da yake kammala jawabin nasa, Yar’adua ya ce wannan biki ya sa ya fahimci cewa shekaru 11 kawai ke tsakanin shi da shekarun NUJ. Ya kuma yaba wa dattawan 'yan jarida da suka halarci taron, yana mai cewa suna da gagarumar gudunmuwa a harkar jarida da ci gaban kasa.

“Ina taya daukacin 'yan jarida da jami’an NUJ murna a wannan rana ta cika shekaru 70. Wannan dama ce ta musamman da za mu duba inda muka fito da kuma inda muka dosa,” in ji shi.

Follow Us