Gwamnatin Katsina Ta Bukaci Jama’a Su Zauna Lafiya da Kwarin Gwiwa Kan Yaki da 'Yan Bindiga

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28072025_144329_IMG-20250728-WA0081.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes 

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana damuwa kan yadda wasu mutane ke yada bayanan karya da tsoratarwa a kafafen sada zumunta, da nufin rage kimar nasarorin da aka samu a yaki da ’yan bindiga a karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Muazu, PhD, ya fitar a ranar Lahadi, gwamnati ta bayyana cewa kafin zuwan Gwamna Radda mulki a 2023, dukkan kananan hukumomi 24 na jihar sun fuskanci matsanancin matsalar 'yan bindiga. Sai dai yanzu, sakamakon dabarun tsaro da hadin gwiwa da hukumomin tsaro, an samu ci gaba mai ma’ana a sassan jihar da dama.

Danmusa ya bayyana wasu Kananan Hukumomin da Aka Cimma Cikakken Zaman Lafiya kamar Jibia, Batsari, Danmusa, Katsina, Batagarawa, Charanchi, Bindawa, Ingawa, Kafur, Danja, da Kusada sun samu kwanciyar hankali gaba daya daga hare-haren 'yan bindiga. Dakta Danmusa yace: Yankunan da Matsalar ta Ragu Amma Har Yanzu Akwai Barazana a Wasu Sassa sun hada da
Malumfashi, Kurfi, Dutsinma, Kankia, Musawa, Bakori, Funtua, Sabuwa da Dandume.

Haka zalika Yankunan da Har Yanzu Matsalar ke Ci Gaba da Faruwa sun hada da Faskari, Kankara, Safana da Matazu.

Sanarwar ta ce, duk da kalubalen da ake fuskanta a wasu yankuna, Gwamna Radda bai tsaya ba, yana ci gaba da karbar rahotanni na tsaro daga manyan jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki koda a lokacin da yake cikin jinya bayan hadarin mota.

Gwamnatin ta koka kan yadda wasu ke amfani da kafafen sada zumunta wajen yada labaran da ba su da tushe ko makama, suna cutar da kokarin jami’an tsaro da kuma rage kwarin gwiwar jama’a.

Sanarwar ta jaddada cewa yaki da 'yan bindiga na bukatar lokaci, tsari da hadin kai, musamman a dazukan da ke da matsanancin hadari. Wannan ne ya sa aka kafa Katsina Community Watch Corps, wadanda ke aiki kafada da kafada da sojoji, ’yan sanda, rundunar sojin sama, da ’yan banga a fadin jihar.

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana damuwa matuka akan yadda ta rasa jami'an tsaro fiye da 130 l, inda ta bayyana adadin wasu da cewa: Fiye da mambobi 100 na Katsina Community Watch Corps sun rasa rayukansu a bakin aiki. Fiye da ’yan sanda 30 sun mutu. Wasu sojoji da dama ma sun bada rayukansu.

Sanarwar ta ce wadannan jarumai sun cancanci girmamawa, ba cin zarafi a kafafen sada zumunta ba. Hakanan, gwamnatin jihar tana ci gaba da tallafa wa wadanda aka kubutar daga hannun 'yan bindiga, wadanda suka jikkata da iyalan wadanda suka rasu.

Gwamnatin ta ce tana kashe makudan kudade don samar da kayan aiki da kwarin gwiwa ga jami’an tsaro. Sai dai nasarar yaki da 'yan bindiga ba daga gwamnati kadai bane, yana bukatar hadin kan kowa da kowa.

Gwamnati na bukatar al’ummar jihar Katsina su kasance cikin natsuwa da hadin kai. Kada su yada labarai marasa tushe, kuma su kasance masu bayar da rahoton duk wani abu da ya saba da doka. An samar da layin gaggawa domin karbar korafe-korafe ko bayanai masu muhimmanci.

A karshe, gwamnatin jihar ta bukaci shugabannin addini da na gargajiya da sauran jama’ar gari da su ci gaba da addu’o’i da goyon baya. Gwamnati ta tabbatar da cewa akwai kalubale, amma jajircewa da himma sun rinjaye shi.

Follow Us