Rashin Magudanar Ruwa Ya na Hana Yara Zuwa Makaranta a Unguwannin Danmada da Tudun Baras A Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28072025_151619_FB_IMG_1753715543618.jpg


Auwal Isah | KATSINA TIMES 

Al'ummar unguwannin Danmada da Tudun Baras da ke cikin mazabar Wakilin Arewa B a karamar hukumar Katsina, sun koka kan yadda rashin magudanar ruwa ke jefa su cikin halin kunci duk lokacin da aka samu saukar ruwan sama.

A cewar al'ummar, ruwan sama na haddasa ambaliya da toshe hanyoyi, lamarin da ke hana yara zuwa makaranta da ma hana mutane gudanar da harkokin yau da kullum, ciki har da bin gawar mamata zuwa makwabtansu.

A cikin wata tattaunawa da suka yi da KatsinaTimes bayan kammala zaman gaggawa da suka kira da yammacin Lahadi, kwamitin da al'ummar suka kafa don fuskantar wannan matsala ya bayyana cewa matsin da suke ciki ya dade yana ci gaba da ta'azzara.

“Duk lokacin da muka ga girgizar hadari, mukan shiga rudani domin ba za mu iya shiga cikin unguwa ko fita ba. Hanyoyin da ke hada Danmada da Tudun Baras duk sukan rufe da ruwa,” in ji Husaini Isiyaku, mazaunin unguwar.

Shi ma Malam Sirajo Yahuza ya bayyana cewa: “Da zarar aka yi ruwa, sai ka zauna gida saboda babu hanyar fita neman abinci. Ruwan daga Dutsin Safe Low-cost yana kwararowa ta Tudun Baras da Danmada, yana jefa mu cikin kunci.”

A cewar Malam Sa’idu Zakiru, jigo a kwamitin al’umma: “Yaranmu ba sa zuwa makaranta idan aka yi ruwa. A rana daya sai ka ga sun zauna gida saboda babu hanyar da za su bi su isa makaranta, musamman makarantar Boko.”

Mai unguwar Danmada, wanda shi ma ya bayyana matsalolin, ya ce: “Idan an samu rasuwa a lokacin ruwa, sai a zauna tare da gawar mamaci har sai ruwa ya tsaya, domin ba za a iya kai gawar makwabtanta ba.”

Al’ummar yankunan sun roki gwamnatin jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda, da ta shiga cikin lamarin domin kawo karshen wannan matsala da ke barazana ga lafiyar su da rayuwar su gaba ɗaya.

“Muna rokon gwamnatin Malam Dikko Radda ta duba wannan matsala da idon rahama. Wannan ruwan da ke shigowa yana rugujewa gidajenmu, saboda babu hanyar da ke kwashe ruwan yadda ya kamata. Wannan matsala ce ta gaggawa,” in ji al’ummar.

Al’ummar sun jaddada cewa magance wannan matsala zai inganta rayuwar su da harkokin ilimi da lafiya a yankin.

Follow Us