Daga Wakilinmu | Katsina Times
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bukaci 'yan Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar da su fito su yi rajistar zama mambobin jam’iyyar, tare da alkawarin samar da gwamnatin da ta haɗa kowa da kowa, da ɗorewar zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki.
A wata sanarwa da Katsina Times ta samu, Sakataren Ƙasa na Riko mai kula da Ƙarfafa Rajista da Wayar da Kai na Ƙasa baki ɗaya, Sanata Sadiq Abubakar Yaradua, ya ce lokaci ya yi da 'yan Najeriya za su rungumi jam’iyyar da ya bayyana a matsayin "jam’iyyar gaskiya da amana."
Sanata Yaradua ya jaddada cewa ADC jam’iyya ce da ta ƙunshi shugabanni nagari masu kishin ƙasa da nufin tabbatar da zaman lafiya, adalci da ci gaban al'umma.
"ADC ba jam’iyyar da ke amfani da ruɗu ko ƙaryar alkawura ba ce. Muna da cikakken shirin farfaɗo da ƙasa ta hanyar gaskiya, mutunci da ɗaukar nauyin al’umma yadda ya kamata," in ji shi.
Ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da gaza cika alkawurran da ta ɗauka, yana mai cewa ta jefa ƙasar cikin ƙunci ta hanyar yaɗa ƙarya da nuna gazawa wajen aiwatar da tsare-tsaren da suka dace.
“Ba kamar shirin ‘Sabon Fata’ na jam’iyyar APC ba wanda mutane da dama ke kallon sa a matsayin hanyar ruɗin jama'a, ADC na da tsari na gaskiya wanda ke da nufin bunƙasa rayuwar 'yan ƙasa cikin gaskiya da adalci,” in ji shi.
Sanata Yaradua ya bayyana ADC a matsayin jam’iyyar da ba ta nuna bambanci ba, wadda ke haɗa kowa da kowa ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba, yana mai cewa jam’iyyar na da burin farfaɗo da martabar Najeriya ta hanyar haɗin kan al’umma da taimakon Allah.
Ya roƙi 'yan Najeriya da su mara wa jam’iyyar baya da yin rajista domin su zama ɓangare na ginin ƙasa, yana mai tabbatar da cewa ADC za ta yi amfani da albarkatun ƙasa don amfanar da dukkan ‘yan ƙasa.
“Lokaci ya yi da za mu rungumi jam’iyya mai gaskiya da burin al’umma. ADC ita ce jam’iyyar makoma wadda za ta dawo da haɗin kan ƙasa da ci gaba mai ɗorewa,” in ji shi.