Tsohon Ma’aikacin Gwamnati Ya Koka Kan Jinkirin Biyan Gratuity Tun Shekarar 2020

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes31072025_185943_FB_IMG_1753988341631.jpg

Daga Katsina Time

Kabir Ahmed A/Kuka, tsohon ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya a jihar Katsina tun daga shekarar 2020, ya bayyana damuwarsa kan yadda har yanzu ba a biya shi haƙƙinsa na Gratuity ba, duk da cika shekaru fiye da huɗu zuwa biyar da ya ajiye aiki.

A cikin wani dogon rubutu da yayi a shafukan yanar gizo ta zamani, Kabir ya bayyana cewa an fara tantance shi a lokacin tsohon gwamna Masari, amma daga baya da ya sake zuwa don tantanceshi a ƙarƙashin wannan sabuwar gwamnati ta Dikko Umar Radda, sai ya samu an yi kuskuren cire sunansa daga jerin waɗanda za a sake dubawa. Wannan kuwa ya jefa shi cikin yanayin damuwa da rashin tabbas tare da sauran abokan aikinsa na gwamnati da suka tsinci kansu a irin wannan hali na tsallake sunayen su. 

“Gaskiya ban so in yi magana ba, amma halin da muke ciki ya tilasta. Na ajiye aiki tun 2020, kuma bayan dogon jira da nayi don a biya ni Gratuity na, sai ga shi an cire sunana daga jerin waɗanda za a sake tantancewa a lokacin da wannan gwamnati ta nemi yin hakan a garon farko. Tun wancan lokaci muka shiga  cikin zullumi da rashin tabbas, kullum cikin rashin barci da damuwa muke tare da iyalanmu,” in ji shi.

Kabir yayi hasashen cewa, akwai yuwuwar su daga cikin waɗanda wannan matsala ta shafa da suka kamu da rashin lafiya, wasu kuwa ƙila sun rasu tun bayan sake tantancewar da aka yi masu watanni uku zuwa huɗu da suka gabata. Ya kuma bayyana cewa akwai rahotannin da ke cewa Gwamna Dikko Umar Radda ya amince da biyan kuɗin, kuma an ce an fitar da su, amma har zuwa 30 ga Yuli da 2025 da yayi wannan rubutu babu wata alama ko sahihiyar sanarwa da ke nuna hakan.

“In har maigirma Gwamna ya bayar da izinin biyan kuɗin, me ke janyo jinkirin fiye da watanni uku ko huɗu? Ina ne kuɗin suka makale? Me ke hana a biya?” in ji Kabir cikin damuwa.

Ya kuma nuna damuwa akan yadda kwamitin da ke kula da biyan kuɗaɗen akan rashin yi masu bayanin halin da ake ciki musamman ganin cewa akwai wakilan tsoffin ma’aikata a cikinsu, wanda ya nuna cewa tamkar ana ƙoƙarin sake jefa su cikin wani sabon yanayin ko neman wasu sabbin takardu daga iyalan su bayan su sun bar duniyar wanda hakan zai zamo ƙara bata wani lokacin. 

“Shin sai an rika tura mu cikin rami ɗaya bayan ɗaya sannan a biya iyalanmu haƙƙinmu? 

A ƙarshe, Kabir ya roƙi Gwamna da kuma masu kusanci da shi da su fahimci halin da wasu daga cikin al’ummar jihar ke ciki, musamman su tsaffin ma'aikata tare da ɗaukar matakin gaggawa domin ganin an biya waɗanda suka ajiye aikin haƙƙinsu.

“Duk wanda ke cikin wannan aikin, ya sani cewa wata rana shima zai tsinci kansa a irin wannan hali. Su ma wadanda suka ajiye din su tuna kafin a biya su sai da suka fuskanci 'yar matsala koda kuwa cikin kwana 3 da ajiye aikin su aka biya su. Ina roƙon Gwamna da duk wani mai ruwa da tsaki acikin batun da a duba wannan lamari da idon rahama,” in ji Kabir Ahmed A/Kuka.

Follow Us