Katsina Times
Malaman addini da kungiyoyin addinai sun hallara domin gode wa Allah da roƙon zaman lafiya a jihar
Kamar yadda aka saba a kowace shekara, gwamnatin jihar Katsina ta shirya babban taron addu’a da ake kira Yaumul Shukr domin nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa ni’imomin da Ya yi wa jihar da kuma roƙon zaman lafiya da ci gaba a tsakanin al’umma.
An gudanar da wannan taro a ranar juma'a, 1 ga watan Agusta, a babban masallacin Juma’a na Danfodiyo da ke Modoji, kusa da gidan gwamnatin jihar Katsina. Taron ya samu halartar fitattun malamai da shugabanni daga manyan ƙungiyoyin addini da suka haɗa da Darika, Izala, Kur'aniyyun, da sauran kungiyoyin addinin Musulunci.
Yaumul Shukr na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Katsina ke ɗauka da muhimmanci, domin tunawa da haɗewar tsoffin lardunan Katsina da Daura wani babban ci gaba da jihar ke ganin ya cancanci a gode wa Allah a kansa tare da roƙon ci gaba da zaman lafiya.
A jawabin rufe taron, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda ya wakilci Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa wannan rana na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a jihar.
“Manufar wannan taro ita ce mu gode wa Allah bisa ni’imomin da ya yi mana, mu roƙi kariya da zaman lafiya, da kuma sabunta alƙawarin mu na ci gaba da gudanar da rayuwa cikin gaskiya da adalci,” in ji shi.
Ya kuma jaddada buƙatar ci gaba da haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin addini, yana mai kira ga malamai da su ci gaba da wa’azi mai gina ƙasa da ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin jama’a.
Taron Yaumul Shukr na ci gaba da zama muhimmin abin tunawa a jadawalin ayyukan jin kai a jihar Katsina, inda ake samun dama ta musamman domin yin addu’o’i, tunani, da kuma neman shiriyar Allah ga gwamnati da al’ummar jihar gaba ɗaya.