Takardun Binciken 'Yan Sanda Sun Kalubalanci Zargin Cewar Gwamnatin Katsina Ta Dauki Nauyin Aikin Hajjin Tsofaffin 'Yan Bindiga

 (Rahoto na Musamman)Takardun binciken 'yan sanda sun nuna cewa wasu daga cikin wadanda ake kira tsofaffin 'yan bindiga da suka rungumi shirin sulhu, wadanda suka je aikin Hajjin shekarar 2026,…

Katsina City News July 27, 2026  ·  12:00 AM
| 156 Views
Takardun Binciken 'Yan Sanda Sun Kalubalanci Zargin Cewar Gwamnatin Katsina Ta Dauki Nauyin Aikin Hajjin Tsofaffin 'Yan Bindiga
Takardun Binciken 'Yan Sanda Sun Kalubalanci Zargin Cewar Gwamnatin Katsina Ta Dauki Nauyin Aikin Hajjin Tsofaffin 'Yan Bindiga

 (Rahoto na Musamman)

Takardun binciken 'yan sanda sun nuna cewa wasu daga cikin wadanda ake kira tsofaffin 'yan bindiga da suka rungumi shirin sulhu, wadanda suka je aikin Hajjin shekarar 2026, sun shaida wa masu bincike cewa su ne suka biya kuɗin Hajjin nasu da kansu, lamarin da ya saɓa wa zargin cewa Gwamnatin Jihar Katsina ce ta dauki nauyin tafiyarsu.


Takardun binciken, waɗanda suka ƙunshi bayanan shaidu, wasiƙun hukuma da kuma martanin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina, sun kasance cikin binciken da Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina ta gudanar bayan zargin da malamin Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dakta Bashir Kurfi, ya yi.


Kurfi ya yi zargin ne a wata hira da aka yi da shi a Trust TV cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta dauki nauyin wasu shugabannin 'yan bindiga domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 a ƙasar Saudiyya.


Zargin ya jawo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasa, inda gwamnatin jihar ta kai ƙara ga 'yan sanda. Daga bisani aka gurfanar da Kurfi a gaban Kotun Majistare da ke Katsina bisa tuhume-tuhumen bata suna da yada ƙarya mai cutarwa. An tsare shi a gidan yari kafin daga baya kotu ta ba shi beli.


Sai dai takardun binciken sun nuna cewa shugabannin al'umma, jami'an ƙananan hukumomi, shugabannin Fulani da kuma alhazan da kansu sun tabbatar wa masu bincike cewa sun biya kuɗin Hajjin ne daga aljihunsu.


Shugaban Kwamitin Sulhu na Ƙaramar Hukumar Danmusa, Salisu Buhari, ya bayyana wa masu bincike cewa Ardo Abdulkarim Abdullahi ya sanar da shi cewa Ummaru Mainore, wanda ya ce yana cikin masu shiga shirin sulhun gwamnati, yana son zuwa aikin Hajji.


A cewarsa, ya sanar da Shugaban Ƙaramar Hukumar Danmusa, Ibrahim Mohammed, wanda daga bisani ya tuntubi Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dakta Nasiru Babangida Mu'azu.


Buhari ya ce daga baya an sanar da su cewa Gwamna Dikko Umaru Radda ya amince a ba su damar ci gaba da shirye-shiryen tafiyar bayan an kammala tantancewar tsaro.


Ya jaddada cewa wannan amincewa ta shafi bayar da izinin tafiya ne kawai, ba wai gwamnatin jihar ce ta biya kuɗin Hajjin ba.


Ya kuma bayyana cewa Ummaru Mainore da Wada Bello, wanda aka fi sani da Wada Yellow Matazu, sun haɗa kuɗi har Naira miliyan 13.394, waɗanda aka biya domin gudanar da dukkanin shirye-shiryen Hajjin kafin tafiyarsu zuwa Saudiyya.


Shi ma Ardo Abdulkarim Abdullahi ya shaida wa 'yan sanda cewa babu wani jami'in gwamnati da ya biya ko ya yi alkawarin biyan kuɗin Hajjin.


Ya ce da ace gwamnatin jihar ta dauki nauyin Hajjin tsofaffin 'yan bindiga, da shi ma yana cikin wadanda za su amfana domin yana da burin zuwa Hajji amma bai samu isasshen kuɗi ba.


Wani ɗan kasuwa mai suna Kamaladin Salisu ya kuma bayyana cewa tsakanin mutum 10 zuwa 11 daga cikin tsofaffin 'yan bindigar tare da matansu sun je Hajjin shekarar 2026 bayan sun biya kuɗinsu da kansu, wasu ma ta hanyar biyan kuɗin a matakai.


Ya ce ya tattara kwafen takardun biyan kuɗin Hajjin wasu daga cikinsu, yana mai cewa duk wanda gwamnati ta dauki wa nauyin Hajji ba ya karɓar irin waɗannan takardun biyan kuɗi.

Advertisement

BSIL Security Report


Haka kuma, Shugaban Ƙaramar Hukumar Safana, Abdullahi Sani Safana, ya shaida wa masu bincike cewa mutum 13 daga yankinsa sun biya kuɗin Hajji da kansu bayan sun samu izinin tafiya daga hukumomin da abin ya shafa.


Ya bayyana zargin cewa gwamnatin jihar ce ta biya musu kuɗin Hajji a matsayin ƙarya da kuma bayanin da ke yaudarar jama'a.


Daga cikin alhazan da suka bayar da shaida akwai Umar Ado Dambafashi, wanda ya ce ya sayar da shanu 11 da kayan amfanin gona domin tara kimanin Naira miliyan 7.5 da ya biya kuɗin Hajjin.


Sauran da suka bayar da irin wannan bayani sun haɗa da Ibrahim Gambo, Ilyasu Mondi, Lawal Ibrahim, Abdullahi Abubakar da Amadu Usman, inda dukkansu suka ce sun samo kuɗin Hajjin ne ta hanyar sayar da dabbobi, amfanin gona, ajiya ko kuma rance.


Domin tabbatar da gaskiyar lamarin, Rundunar Binciken Laifuka ta Jihar Katsina (SCID) ta rubuta wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina wasiƙa tana neman bayanan alhazan da kuma kwafen takardun biyan kuɗinsu.


A martanin da hukumar ta bayar, ta tabbatar da cewa dukkan mutane 15 da aka ambata sun yi rajista ta hukuma, sun biya cikakken kuɗin Hajji kuma sun gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 ta hannun hukumar.


Har ila yau, hukumar ta miƙa wa 'yan sanda kwafen takardun biyan kuɗin Hajji, bayanan fasfo da kuma bizar Saudiyya domin taimakawa binciken.


Takardun binciken sun kuma nuna cewa 'yan sanda sun gayyaci wasu jami'an gwamnati da shaidu, ciki har da Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Danmusa, Zaharaddeen Umar, da wasu daga cikin alhazan domin su ba da bayanansu.


Bayan samun belinsa, Dakta Bashir Kurfi ya ci gaba da cewa abin da ya yi shi ne gabatar da zargi wanda ya kamata a bincika, maimakon gurfanar da shi a kotu. Ya kuma soki yanayin da ya tarar a Gidan Gyaran Hali na Katsina lokacin da yake tsare.


Majiyoyi sun ce bayan dawowarsu daga Saudiyya, wasu daga cikin tsofaffin 'yan bindigar da abin ya shafa sun fuskanci tambayoyi daga 'yan sanda kafin daga bisani a sake su.


Takardun binciken ba su nuna cewa masu binciken sun gano wata hujja da ke tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Katsina ce ta biya kuɗin Hajjin mutanen ba.

Sai dai lamarin ya ci gaba da haifar da muhawara kan shirin sulhun gwamnati da tsofaffin 'yan bindiga, tare da kira ga ƙarin gaskiya, riƙon amana da bayyana bayanai ga jama'a.

A halin yanzu, shari'ar da ake yi wa Dakta Bashir Kurfi na gaban kotu


Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 8?