Mu’azu Hassan @Katsina Times
Jaridar Katsina Times ta gudanar da wani zaben gwaji domin tantance ra’ayin al’umma kan ‘yan takarar kujerun Sanatoci a yankunan Katsina, Funtua da Daura.
Mun gudanar da wannan bincike ne ta hanyar jin ra’ayin jama’a a tsakanin ƙananan hukumomin da ke cikin yankunan sanatocin, domin gano yadda al’umma ke kallon ‘yan takarar da ke neman kujerun.
Wannan zaben gwaji ne kawai, kuma ba wai sakamakon zaɓe na ƙarshe ba ne. Saboda haka, komai na iya sauyawa kafin lokacin zaɓe. Sai dai ga abin da bincikenmu ya nuna a halin yanzu:
Yankin Sanatan Funtua:
A wannan yanki, Sanata Muntari Dandutse na jam’iyyar APC ne ke kan gaba a cikin waɗanda aka tambaya, inda yake gaban abokan hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Nura Khalil, da Jamilu Muhammad na jam’iyyar ADC.
Yankin Sanatan Katsina ta Tsakiya:
A Katsina ta Tsakiya, Hamisu Gambo na jam’iyyar PDP ne ke kan gaba, yayin da yake gaban Kanar Abdul’aziz Musa Yar’Adua na jam’iyyar APC, da kuma ɗan takarar da jam’iyyar ADC sanata Abubakar Saddiq "yar adua
Yankin Sanatan Daura:
A yankin Daura kuwa, idan har Alhaji Lawal Daura ne zai tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, binciken ya nuna cewa yana kan gaba a cikin waɗanda aka tambaya, inda yake gaban Alhaji Nasiru Yahya na jam’iyyar APC, da kuma ɗan takarar da jam’iyyar PDP ta tsayar.
Binciken da muka gudanar ya dogara ne kan tsarin tambaya da amsa, inda aka nemi ra’ayin mutanen da aka tuntuɓa tare da dalilan da suka sa suka zaɓi ɗan takarar da suka nuna goyon baya.
binciken ra’ayin jama’a ne na gwaji, . Ra’ayin jama’a na iya sauyawa a kowane lokaci kafin a kai ga zaɓe.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page.katsina city news
Facebook page.jaridar Taskar labarai
All social media handles @ katsina times
07043777779


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!