Gwamnatin Katsina Ta Shirya Gasar Sallah Don Tallafa wa Matasa da Raya Al’adu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes10062025_233113_FB_IMG_1749598154653.jpg

Gwamnatin Katsina Ta Shirya Gasar Sallah Don Tallafa wa Matasa da Raya Al’adu

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina TIMES

Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya babban bikin wasannin Sallah da na al’adu mai taken "X-Games Keke Reloaded" domin karfafa gwiwar matasa, hada kan al’umma da kuma raya al’adun gargajiya na jihar.

An gudanar da bikin ne a ranar Litinin, 9 ga Yuni, 2025, karkashin jagorancin Hukumar Tarihi da Al’adu ta Jihar Katsina, tare da kulawar Shugaban Ma’aikatan Gwamna, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir da kuma Darakta Janar na Hukumar, Dr. Kabir Ali Masanawa.

Bikin ya kunshi hadin gwiwar wasannin zamani da na gargajiya, inda ya ja hankalin dubban mutane daga sassa daban-daban na jihar. Daga cikin manyan abubuwan da suka dauki hankalin jama’a akwai gasar tseren keke da gasar Mashin mai kafa uku (Keke NAPEP), wadda ta fara daga gadar Play-Over a Tashar Bala zuwa Filin Wasan Muhammadu Dikko a hanyar Mani. Tseren mai tsawon fiye da kilomita 10 ya gudana cikin tsari tare da sa ido daga jami’an tsaro, ma’aikatan lafiya da masu kula da wasanni.

Domin tabbatar da hada kowa da kowa, an gudanar da wasannin nakasassu irinsu tseren keken guragu da (parasoka) (kwallon hannu na masu nakasa). An bai wa wadanda suka yi nasara kyaututtuka da dama, ciki har da sabon Keke NAPEP ga wanda ya lashe gasar keken NAPEP, da kuma ₦500,000 ga wanda ya ci gasar tseren keke. Wadanda suka zo na biyu da na uku suma sun samu kyaututtukan kudi da takardun girmamawa.

Bikin ya kuma kasance wata dama ta nuna al’adun gargajiya na Katsina, inda aka gabatar da Hawan Daba wanda ke nuna tarihi da girman masarautar Katsina, kokowa, wasannin dabbobi da suka hada da kura, biri da macizai, wasan wuta, rawa a kan Kekuna da kuma wakoki da raye-rayen gargajiya. Duk wadanda suka halarta suka kuma nuna bajinta a fannin al’adu sun samu kyaututtuka da lada mai tsoka.

Wasu manyan ‘yan siyasa irin su Sanata Muntari Dandutse da Dan Majalisar Wakilai, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da Shehu Dalhatu Tafki duk sun bayar da gudunmowarsu ta hanyar ba da motoci biyu na NAPEP Mashina, da kuma tallafin kudi daga mutane daban-daban domin nasarar bikin.

Gwamna Dikko Umaru Radda (PhD) ya sha jaddada kudurin gwamnatinsa na ci gaba da ba da muhimmanci ga cigaban matasa da raya al’adu. Ya ce wasanni da al’adu na daga cikin manyan hanyoyin da ke hada kan al’umma da kuma wayar da kai ga matasa game da muhimmancin tarihin su.

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Katsina ta kafa wani kwamitin masana tarihi karkashin jagorancin Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida, domin gano da kuma farfado da wuraren tarihi da za su kara bunkasa yawon bude ido da wayar da kan jama’a kan tarihin Katsina.

Ta hanyar irin wannan shiri na X-Games Keke Reloaded, Jihar Katsina na zama abin koyi wajen hadin gwiwar wasanni da al’adu domin gina cigaba, hadin kai da alfaharin jiha.

Follow Us