Daga Ɗanjuma Katsina
A wannan makon duk wani gidan jarida da kafar sadarwa a duniya ba labarin da suke bayarwa kamar na wani jirgin ruwa da ke ɗauke da masu fafutuka su sha biyu da suka sha alwashin karya lagon takunkumin da aka soja da gwamnatin Isra'ila ta sanya na kai abinci ga mutanen Gaza sama da mutane miliyan biyu da suke fama da ƙuncin yunwa, rashin abinci da ƙarancin magunguna.
Wannan jirgi wata matashiya ke jagorantar tafiyar mai suna Greta Thunberg.
Tafiya ce mafi hatsari da aka sani a duniya. A baya an taɓa jaraba irin ta sojan Isra'ila suka auka wa jirgin har suka kashe mutane tara.
A kwanan nan da aka yi ƙoƙari irin bam ya tashi a cikin jirgin da aka yi niyyar tafiyar dole aka dakatar.
Wannan karon Greta Thunberg da masu mara mata baya su 11 suka sha alwashin sai sun ƙarasa tafiyar.
Ƙasar Isra'ila da ƙawayenta sun yi gargaɗi da jan kunne a bayyane a kan hatsarin tafiyar, Greta suka sa alwashin sai sun yi tafiyar.
Jirgin ruwa suka samu mai ɗaukar mutane 20, amma su 12 ke ciki, sai wani ɗan jarida da mai ɗaukar masa hoto daga talabijin na ALJAZEERAH.
Masu fafutukar sun sayi kayan abinci da kayan buƙatar jarirai da kuma magunguna suka ce suna son su kai wa mutanen Gaza da ke cikin uƙuba.
Sun ce kayan ba wasu kaya ba ne, amma suna son nuna tausayawarsu a aikace ga mutanen Gaza, suna kuma son nuna masu a aikace duniya na tare da su, an kuma san halin da suke a ciki.
Masu fafutukar sun maƙala kyamarori a cikin jirgin don watsawa kai tsaye yadda tafiyar tasu ke gudana. Miliyoyin mutane suka riƙa bin su kai tsaye ta yanar gizo a kan yadda suke tafiyar tasu.
Sojan Isra'ila sun yi, sun yi su datse duk wata sadarwa da jirgin, amma abin ya gagara.
Kowane minti duniya na kallon yadda jirgin ke tafiya a cikin teku da yadda waɗanda ke cikin jirgin ke rayuwarsu.
Isra'ila ta yi duk ƙoƙarinta na datse sadarwa tsakanin jirgin da mutane, abin ya ci tura.
Zanga zangar ta farko aakan ɗumamar yanayi a gaban majalisar dokokin Sweden tana yar shekaru sha biyar
Sojan Isra'ila sun auka wa jirgin, tare da kama shi, kilomata 160 kafin su isa Gaza. Daga nan ne aka daina samun saƙon jirgin kai tsaye, sai abin da Isra'ila ta ce a kan jirgin da mutanen da ke ciki.
Isra'ila sun sanar cewa, sun karkata jirgin zuwa tashar jiragen ruwa ta Ashkelon, kuma za a yi wa masu fafutikar tambayoyi a kuma nuna masu wani fim da aka tsara na yadda aka ce Hamas sun kai wa Isra'ila hari a ranar 9 ga Oktoba, 2023.
Yanzu labari a kan waɗannan masu fafutukar sai abin da Isra'ila ta ce. Sai kuma in sun samu 'yancinsu su ba da cikakken rahoto.
A ranar talata 10/6/2025 an saki greta da mutane uku aka kuma tasa keyar ta zuwa kasar su Sweden.Tana sauka birnin faris ta fara da caccakar Israela da kuma tausayawa ga halin da mutanen Gaza ke a ciki.
Sauran mutane takwas an kaisu wata kotun Israela da cigaba da tsare su.
Wannan tattakin nasu greta ya kara zaburar da duniya akan halin da mutanen gaza ke ciki.
Wanda yanzu haka ya jawo wasu mutane a kasashen Tunisiya, Algeria, Libya da Masar na kan hanyarsu na zuwa Gaza ko ana ha maza ha mata.
Wadda ta jagoranci wannan tafiya, wadda sunanta shi ne ya yi ta amo a duniya, ita ce Greta Thunberg.
Yarinya ce mai shekaru 22 a duniya. Asalinta 'yar ƙasar Sweden ce. Tana da shekaru 15. Ta fara magana a kan matakin da ƙasarta ya kamata ta ɗauka a kan canji da ɗumamar yanayi a duniya.
Ta fara bore na ƙin zuwa makaranta duk ranar Juma'a don ta jawo hankalin ƙasarta a kan amfani da wasu ma'adanai da za su iya cutar da yanayi da kuma kawo ɗumamar yanayi a duniya.
Ta yi zanga-zanga ita ɗaya a gaban majalisar dokokin na ƙasar Sweden.
Waɗannan ayyukan nata ya sanya duniya ta fara jin labarinta da sauraren wane saƙo take ɗauke da shi.
A 2018 ta je har Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi magana a kan hatsarin ɗumamar yanayi a duniya.
A 2019 ta yi tafiya a wani jirgin ruwa wanda bai amfani da ma'adanai masu kawo ɗumamar yanayi daga ƙasar Ingila zuwa New York, kuma ta sake magana mai zafi ga shugabannin ƙasashen duniya a kan hatsarin ɗumamar yanayi a duniya.
A 2023 bayan ta kammala babbar makaranta fafutukar ta canza salo zuwa magana da yawun waɗanda ake cin zalin. Wannan ya kai aka fara kama ta, tsare ta da kai ta kotu.
Ta riƙa bayyana goyon bayanta ga al'ummar Palastinu kai tsaye da kuma koke a kan halin da suke ciki.
Manyan jaridu a duniya sun misalta ta da matashiya mafi tasiri a duniya. Jaridu irin su GUARDIAN ta birnin London, TIME ta Amurka da mujalla FORBES an kuma ba da sunan domin yiyuwar ba ta lambar yabo ta zaman lafiya ta duniya ta Noble Peace Prize.
Wannan matashiya abar ɗaukar darasi ne ga rayuwarta da gwagwarmayarta ga matasanmu maza da mata.