Auwal Isah Musa | Katsina TIMES
Shugabar Hukumar Ilimin Manya ta Jihar Katsina, Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai, ta roki ‘yan majalisar jiha da na tarayya da su mara wa hukumar baya domin ceto al’umma daga duhun jahilci da kuma farfado da harkar ilimin manya a fadin jihar. Ta ce irin wannan goyon baya zai taimaka wajen rage nauyin da ke kan Gwamna Dikko Radda a fannin ilimi.
A wata fira ta musamman da ta yi da manema labarai ciki har da Katsina Times, Hajiya Kaikai ta bayyana yadda ta kudurta aniyar dawo da martabar hukumar da kuma bunkasa ilimi a yankunan karkara, musamman ga manya da ba su samu damar karatu ba.
Ta bayyana cewa da zuwanta ofis, abu na farko da ta yi shi ne ziyarar ban girma ga Sarakunan Katsina da Daura, inda ta gabatar da irin tsare-tsaren gwamnatin Radda na farfado da ilimi, musamman a bangaren manya da hukumar ke da alhakin kula da shi.
Ta ce tsarin da hukumar ke aiki da shi bai tsaya akan karatun Boko kadai ba, har da na addinin Musulunci da kuma na koyar da sana’o’i, wadanda za su amfani maza da mata baki daya.
“Ayyukan sana’o’in da muke koyarwa za su rage rigingimu tsakanin miji da mata, za su rage mace-macen aure domin matan za su samu dogaro da kai da kuma taimaka wa mazajensu,” in ji ta.
Hajiya Kaikai ta jaddada cewa jahilcin da hukumar ke yaka ba karamin kalubale ba ne, domin shi ke haddasa mafi yawan matsalolin da ake fuskanta a kasar nan. “Jahilci na daga cikin abubuwan da ke haddasa tabarbarewar tsaro a wannan kasa,” in ji ta.
Dangane da tsarin bunkasa hukumar, ta ce ta tura daraktoci a fadin kananan hukumomin jihar domin su duba halin da cibiyoyin koyar da manya da kuma 'Women Centre' ke ciki.
“Tun zuwana yanzu mun bude sababbin azuzuwan karatu 68 a gidajen Hakimai. Jimillar azuzuwan da muke da su yanzu a fadin jihar Katsina sun kai 1,666,” in ji Hajiya Kaikai.
Ta ce saboda ziyartar makarantu da suke yi yanzu, hatta Malaman makarantar allo suna nuna bukatar a bude musu makarantun Boko don su koyi yadda ake mu’amala da na’urori irin su waya, domin da dama daga cikinsu ba su iya sarrafa su yadda ya kamata ba.
Ta ce malamai a kananan hukumomi sun nuna farin ciki da ziyarar da suka fara samu yanzu daga hukumar, domin a cewarsu tun da aka bude cibiyoyin ba a taba kula da su ba sai zuwanta.
“Ni kuma kasancewata mace ta farko da ta jagoranci wannan hukuma, na dauki hakan a matsayin kalubale gare ni domin na tabbatar mun samu nasara,” in ji ta.
Sai dai ta ce duk da ci gaban da ake samu, har yanzu hukumar ba ta da isasshen kayan gudanarwa. Ta roki gwamnati da ‘yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi da su kara azama wajen tallafa wa hukumar da kudade da kayan aiki.
“Idan aka ba ni dama da kayan aiki, zan jagoranci shiga ko da rugagen Fulani inda ake fama da matsalolin tsaro domin koyar da ilimi. Domin illar jahilci ce ke janyo wadannan matsalolin,” in ji ta.
“Idan aka ilmantar da su da ‘ya’yansu, wallahi komai zai sauya. Za mu ga alherin wannan hukuma ya bayyana sosai,” ta kara da cewa.
A nasu bangaren, wasu daga cikin daraktocin hukumar sun bayyana farin cikinsu da irin sauyin da aka samu tun bayan zuwan Hajiya Kaikai. Sun ce rabon da su ga irin wannan ci gaba tun kusan shekaru 7 zuwa 8 da suka wuce.
“Zuwanta ya sa mun shiga gidajen gyaran hali don duba yadda ake koyar da fursunoni, wanda kafin zuwanta ba mu taba yin hakan ba,” in ji Hasan Umaru, Darakta mai kula da hulda da jama’a.
Ya bukaci gwamnatin jihar da ta samar da motocin hawa domin saukaka zirga-zirga ga ma’aikatan hukumar.
“Mun zauna a wannan hukuma tsawon shekaru, amma kamar ana zube. Da zuwanta kowa ya san aikinsa, komai ya dawo yadda ya kamata,” in ji Bilkisu Abdullahi Yusuf, daraktar shirin ‘Women Program’.
Binta Balan Goggo, daraktar sashen kulawa da aiwatarwa, ta yaba da bude sababbin cibiyoyin koyarwa a gidajen Hakimai.
Rakiya Sada Abdullahi, daraktar sashen 'Literacy', ta ce: “Ayyukan da Hajiya Bilkisu ke yi, har ma wasu mazan da suka gabace ta ba su yi irin hakan ba. Muna godiya ga Gwamna bisa zabo ta a matsayin shugabarmu. Haka kuma muna rokon gwamnati da ta kara kudin alawus din da ake biyan malamai, domin dan abinda ake basu bai wuce na hawan babura ba."