An Daura Auren Diyar Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29062025_072431_FB_IMG_1751181717200.jpg


A ranar Asabar, 28 ga watan Yuni, 2025, an gudanar da daurin auren Asma’u Abdullahi Aliyu, ‘ya ga Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua, a cikin wani gagarumin biki da ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban.

An gudanar da daurin auren ne a masallacin Juma’a na Banu Commassie da ke unguwar GRA a birnin Katsina, inda Liman Surajo Muhammad Kankiya ya jagoranci addu'ar daurin auren tsakanin Asma’u Abdullahi da Murtala Isa Girka, akan sadaki naira 200,000.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ‘yan uwa, abokan arziki da sauran al’umma. Cikin wadanda suka halarta akwai Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda ya bayyana farin cikinsa da kuma fatan alheri ga sabbin ma’auratan.

Sauran manyan baki sun hada da Shugaban Ma’aikata na Jiha, Alhaji Falalu Bawale; Kwamishinan Yada Labarai, Dr Bala Salisu Zango; dan majalisar tarayya mai wakiltar Mashi–Dutsi, Hon. Salisu Yusuf Majigiri; da tsohon mataimakin gwamnan jihar Katsina, Barista Surajo Umar Ɗanyaro Damari.

Haka zalika, kwamandan hukumar kare haddura na jihar Katsina, Maxwell Kaltungo Ledai; kwamandan hukumar kashe gobara ta tarayya a jihar, Aliyu Abdullahi; mambobin majalisar zartaswa ta jiha; manyan sakatarori da shugabannin sassa da cibiyoyin gwamnati sun halarci taron.

An kuma samu wakilcin mai martaba Sarkin Katsina, ta hannun Madawakin Katsina, Alhaji Hamza Duwan.

Shugabannin kafafen yada labarai, ciki har da shugaban jaridun Katsina Times da Taskar Labarai, Malam Danjuma Katsina, da sauran ‘yan jaridu, malaman jami’o’i, shugabannin kungiyoyin matasa, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, malamai da sauran jama’a sun halarci wannan taron mai albarka.

A cikin jawabinsa, Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua ya nuna godiya ga dukkan mahalarta bisa nuna soyayya da kulawa da suka yi, inda ya roƙi Allah ya sanya albarka a rayuwar sabbin ma’auratan, ya basu zaman lafiya da zuriyya ta gari.

Bikin ya gudana cikin kyakkyawan yanayi na farin ciki, addu’o’i da nishadi, yayin da al’umma suka hadu wajen taya iyalan murnar wannan muhimmin mataki na rayuwa da Asma’u Abdullahi Aliyu ta dauka.

Follow Us