@ katsina times
Malaman makarantun Allo, sunyi watsi da taron gyara makomar almajirai da akayi, jiya kuma sunce shirin ba zaiyi nasara ba.
Sun kira shirin na wani dan boko dan kwangila dake neman samun kudin shiga a wajen gwamnati jahar katsina kuma yayi nasarar hakan. Sunce nawa aka kashe kuma me aka cimmawa?
Malaman Suna magana ne da suka kawo ziyara a ofishin katsina times da safiyar yau Talata.
Sun ce shirin da kashi 98 na malaman wata akida ne wanda dama sun yi shekara da shekaru suna adawa da karatun allo, malaman suka ce wadanda aka tara, Sun yi shekaru suna kafirta su da uwayensu da kakanninsu.
Malaman suka ce, kuma kashi 99 na masu magana ba yan jahar katsina bane , basu santa ba basu san tsarinta ko dabi unta ba.
Malaman suka ce a duk Najeriya, ba kasa mai tarihin ilmin addini musulunci kamar kasar katsina. Sun yi kira ga gwamnatin katsina ta bibiyi wani littafin mai suna Islam and Historian of learning in katsina, Wanda Dakta tsiga da Abdalla suka buga shekaru talatin da suka wuce, zasu ga wacece katsina da wani dan bokon malami zai zo ya fada mana yadda zamuyi.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page; katsina city news
07043777779