Taron sasanci da "yan bindiga HAYA AKA DAUKO MU, MU HALARCI TARON

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09112025_093909_FB_IMG_1762681139226.jpg


..Binciken katsina times 
Wasu "yan bindiga da suka halarci taron sasancin da akayi na kananan hukumomin Batagarawa,charanci.
Sun bayyana ma jaridun katsina times da suka je taron cewa sufa haya aka dauko su, domin su cika benci da cika wuri domin a gansu a wajen taron da bindigunsu.
Jaridun katsina times sun lura da cewa "yan bindigar wasu "yan kwarorin matasa ne da bindigu a hannunsu.kuma taron baida wani karsashi da kwarjini kamar wanda aka Saba yi.
Sannan da alamar tambayar cewa yanzu wadannan sune ke addabar kananan hukumomin uku da hare hare?
Wannan dalilin yasa jaridun katsina times suka fara tambayar "yan bindigar a gefe, ina "yan uwanku? Ya baku zo da yawa ba? Ina makamanku?
 "Yan bindigar sun fada ma jaridun katsina times cewa, mufa haya aka dauko mu..wasun mu ba , ba barayi bane a daji an bamu bindiga ne akace muzo.
"Yan bindigar sun fada ma jaridun mu cewa, da yawan "yan uwanmu da basu zo ba, suna daji suna da tambayoyi akan taron ,rashin basu amsa,
 ya sa suka ce basu zuwa.
Taron dai anyi shi amma kamar yadda jaridun katsina 
Times suka ji kuma suka gani akwai lauje cikin nadi.
Katsina times 
@ www.katsinatimes.com 
Facebook. Katsina city news 
Facebook. Jaridar Taskar labarai
All social media handles. Katsina times 
07043777779.

Follow Us