…Jaridun Katsina Times Sun Gano Maku
Daga Danjuma katsina
@ www.katsinatimes.com
Jaridun Katsina Times sun gano cewa duk mai buƙatar baitocin waƙa daga Alhaji Dauda Adamu Kahutu (Rarara) dole ne ya tanadi miliyoyi masu yawa, ba wai labari ba.
Jaridun Katsina Times sun samu cikakken jerin farashin da Rarara ke caji daga wata takarda da ake rabawa duk wanda ke son a yi masa waƙa.
A cikin takardar an tabbatar cewa duk wanda yake son a yi wa shugaban ƙasa waƙa zai biya Naira miliyan 60. Duk Gwamna ko wanda ke son a yi masa waƙa kuwa, Naira miliyan 40 ake buƙata. Waɗannan sune kuɗin waƙa guda ɗaya.
Idan shugaban jam’iyya na ƙasa ake son a yi wa waƙa, farashin ya tsaya a Naira miliyan 30. Waƙar ɗan majalisar tarayya ko ɗan majalisar dokokin jiha kuwa farashinsa shi ne Naira miliyan 25.
Idan Rarara zai yi maka waƙar buki, to sai ka tanadi Naira miliyan 15. Amma idan waƙar talla ce ta siyasa, ba ya ɗaga garayarsa sai ya tabbatar Naira miliyan 25 sun shiga lalitarsa
Rarara na halartar taruka, amma ba kyauta ba. Waƙar da zai yi a taron siyasa miliyan 30 ce, ba ragin ko ficika.
Idan taron naɗin sarauta ne, kuma kana son a saurari muryarsa, sai ka ajiye masa miliyan 25 a ƙasa.
A ɓangaren bukin aure, Rarara na yin ragi inda zai yi waƙa kan miliyan 15. Amma tallace-tallacen kamfanoni kuwa, sai ka shirya miliyan 20 idan kana son amfani da zazzaƙar muryarsa da baitocinsa.
Waƙar bidiyo ma tana da nata farashin daban. Waƙar siyasa a bidiyo ƙila da zankaɗa-zankaɗan 'yan mata suna rangwaɗa sai ka dire masa Naira miliyan 25.
Waƙar naɗin sarauta a bidiyo ita ce miliyan 15, yayin da waƙar tallace-tallace a bidiyo ke kai wa Naira miliyan 20.
Binciken Katsina Times ya gano cewa Rarara kan yi waƙa ta ganin dama kyauta, ga wanda yake so, musamman in har mutum ya burge shi, ko kuma wani mutunci da ka yi masa. Misali, waƙar Fatima Mai Zogale ya yi ta ne kyauta, kamar yadda wasu abokansa suka shaida wa jaridarmu.
Wasu ma sun ce har waƙar da ya yi wa FMK, mai shagon sayar da atamfa da shaddodi, ita ma a “alakoro” aka yi ta, ko ranyo ba ta biya ba.
Binciken ya kuma gano cewa ko da ka biya kuɗinka, dole ka nemi alfarmar a fitar da waƙarƙa cikin lokaci.
Mun yi iyakar ƙoƙarin jin ta bakin Rarara ko ofishinsa, amma haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.
Duk da haka, majiyoyi daban-daban sun tabbatar mana da farashin, duk da cewa ana iya samun rangwame musamman idan Amarya Hajiya A'isha Humaira ta sa baki.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Facebook: Katsina City News
Katsina times @ all social media handles
Facebook: Jaridar Taskar labarai
07043777779.