FUTD Ta Kammala Horo na Musamman a Kasar Sin Don Inganta Sufurin Jirgin Kasa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08122025_082938_FB_IMG_1765182284573.jpg


KatsinaTimes 

Tawagar Jami’ar Sufuri ta Gwamnatin Tarayya Daura (FUTD) ta kammala wani cikakken horo na musamman a kasar Sin, wanda aka tsara domin kara inganta kwarewa da fasaha a bangaren gudanar da sufurin jirgin kasa a Najeriya.

An gudanar da horon ne a biranen Beijing da Suzhou daga 20 ga Nuwamba zuwa 4 ga Disamba, 2025, karkashin jagorancin kamfanin China Railway Signal and Communication International Co. Ltd. (CRSCI), wanda ke daga manyan kamfanonin kasar Sin da ke samar da tsarin sadarwa da na’urorin zamani na zirga-zirgar dogo.

Mataimakin Babban Manajan CRSCI, Mista Yin Yungong, ya tabbatar da cewa kamfanin zai ci gaba da aiki tare da Najeriya wajen bunkasa tsarin sarrafa harkokin jirgin kasa ta hanyar sabbin fasahohi da horas da kwararru.

Shugaban tawagar Najeriya, Shugaban Jami’ar FUTD, Hon. Farfesa Umar Adam Katsayal, MNI, ya yaba wa CRSCI kan yadda suka gudanar da horon cikin kwarewa. Ya ce ilimin da aka samu zai taimaka wajen cika kudirin jami’ar na gina hazikan masana da za su kara habaka fannin sufuri da gyaran titin dogo a Najeriya.

Follow Us