.
Auwal Isah Musa | Katsina Times
Karamar hukumar Katsina ta kaddamar da Cibiyar Koyon Ilimin Fasahar Zamani (Digital Learning Centre) domin amfanin dalibai da sauran al’ummar yankin.
Bikin kaddamarwar wanda aka gudanar a ranar Litinin a gaban sabon ginin cibiyar da ke cikin Makarantar Firamare ta Muhammadu Dodo Layout a yankin Kudu II, an bayyana wurin a matsayin na saukaka karatu da bunkasa ayyukan al’umma ta hanyar amfani da kwamfuta da yanar gizo.
A jawabinsa, Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Nijeriya (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi, wanda ya samu wakilcin Shugaban Hadin Gwiwar Cibiyar da NITDA, Alhaji Bashir Ibrahim, ya bayyana cewa cibiyar ba kawai wurin koyon ilimin digital ba ce, har ma wani wuri ne na bunkasa ci gaban al’ummar karamar hukumar da jihar baki ɗaya, yana mai cewad "Muna fatan matasa da yara masu tasowa za su ci moriyar wannan wuri na fasaha don kara bunkasa harkokin ilimi da karatunsu."
A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar, Honorabulu Isah Midad, wanda ya jagoranci aikin samar da dakin karatun, ya ce an assasa wannan cibiya don al’umma da yara masu tasowa su samu ilimin kwamfuta.
"Duniyar ta canja, kuma yanzu tana kan yanar gizo; idan ba mu shirya ba, za ta bar mu a baya." In ji shi
Midad, ya kara da cewa duk da cewa karamar hukumar Katsina na daya daga cikin kananan hukumomi masu samun kaso mafi kankanta, amma ta zabi yin wannan dakin karatu na zamani domin ya zama abin koyi ga sauran kananan hukumomi 34 a jihar.
AGwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, wanda yankasance bako mai jawabi a wajn kaddamarwar, ya yaba wa shugaban karamar hukumar kan wannan gagarumin aiki.
"Wannan aiki zai taimakawa matasa maza da mata wajen koyon kwamfuta da sarrafa ta. Muna kira ga sauran shugabannin kananan hukumomi su yi koyi da irin wannan tunani." In ji shi.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma musamman matasa da su mori wannan cibiya ta zamani domin amfana da ilimin zamani da Intanet ke bayarwa, yana mai cewar, "Duniyar ta canja, don haka dole ne mu koyi wannan fasaha cikin lokaci."
Taron kaddamarwar ya samu halartar Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, wasu ‘yanmajalisar zartaswar jihar, kansiloli, masu ruwa da tsaki na karamar hukumar, da sauran al’umma.