Anyi Bikin Cika Shekaru 100 na Kwalejin Dikko, Gwamnati da Tsoffin Ɗalibai Sun Sabunta Ƙudirin Tallafa wa Ilimi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes27122025_165338_FB_IMG_1766854338255.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 27 Disamba, 2025

Gwamnatin Jihar Katsina tare da tsoffin ɗalibai, sarakunan gargajiya da manyan ‘yan Najeriya sun hallara a Dakin Taro na Kwalejin Dikko domin bikin cika shekaru 100 da kafuwar Kwalejin Dikko, Katsina, inda aka bayyana makarantar a matsayin ginshiƙi mai tarihi wajen gina shugabanci da inganta ilimi a Arewa da Najeriya baki ɗaya.

Da yake jawabi a madadin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Mataimakin Gwamna, Malam Faruq Lawal Jobe, ya ce bikin cika shekaru 100 ba taron haɗuwa ba ne kadai, illa murnar tarihin shekaru ɗari na nagarta, hidima da tasiri mai ɗorewa.

Ya bayyana Kwalejin Dikko a matsayin ɗaya daga cikin manyan makarantun sakandare a Najeriya, yana mai cewa tsawon shekaru makarantar ta samar da shugabanni da suka yi fice a fannonin hidimar jama’a, mulki, ilimi, lafiya, injiniya, tsaro, kasuwanci da jagorancin al’umma.

“Duk inda aka ambaci Katsina, ana ganin tasirin Kwalejin Dikko,” in ji Mataimakin Gwamnan, yana jaddada cewa makarantar ba ta tsaya kan takardun shaidar karatu kaɗai ba, sai dai kan tarbiyya, ladabi, kishin ƙasa, jajircewa da hidima.

Malam Jobe ya yabawa Kungiyar Tsoffin Ɗalibai bisa haɗin kai da gudummawar da suke bayarwa ta fannonin koyarwa (mentorship), tallafin karatu, gine-gine da bayar da shawarwari kan manufofi, yana mai bayyana haɗin gwiwar da ke tsakanin tsoffin ɗalibai, shugabancin makaranta da gwamnati a matsayin abin koyi da ya kamata a ƙara ƙarfafa.

Ya kuma tabbatar da cewa ilimi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ta sa a gaba, inda ya bayyana cewa sama da Naira biliyan 100 aka kashe a ɓangaren ilimi tun bayan hawar gwamnatin.

A cewarsa, daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnati akwai gyara da faɗaɗa gine-ginen makarantu, inda aka gina makarantu 152 ƙarƙashin shirin AGILE kashi na 1 da na 2, ciki har da makarantu na musamman a kowace shiyya ta sanata uku. Ya ce an ɗauki malamai 7,325, an horas da sama da malamai 20,000, tare da samar musu da kayan koyarwa na zamani, musamman na fasahar sadarwa (ICT).

Mataimakin Gwamnan ya ƙara da cewa an ɗaukaka Sashen Ilimin Sana’o’i da Fasaha zuwa cikakkiyar Ma’aikatar Ilimin Sana’o’i da Fasaha ta Gaba, sannan gwamnati na daukar nauyin dalibai 109—dukansu ‘ya’yan makarantun gwamnati—da ke karatu a fannoni irin su likitanci, basirar wucin-gadi (AI) da ilimin halittar ƙwayoyin cuta (biotechnology) a ƙasashen Masar da China, tare da cikakken tallafin kuɗin karatu, masauki da alawus.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta ƙarfafa gina ƙwarewar ma’aikata a harkar mulki, tare da tabbatar da adalci a wakilci, inda a yanzu dukkan ƙananan hukumomin jihar ke da akalla sakataren dindindin guda.

“Yayin da gwamnati ke taka rawarta, muna ƙarfafa tsoffin ɗalibai su ci gaba da tallafa wa makarantar ta fuskar ɗabi’a, ilimi da dukiya, su rika ba da shawarwari ga ɗalibai na yanzu, tare da haɗa kai da gwamnati wajen gina shugabannin gobe,” in ji shi.

A nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Tsoffin Ɗaliban Kwalejin Dikko, Alhaji Aliyu Balarabe Saulawa, wanda sakatarensa Aliyu Habibu Dutsinma ya wakilta, ya kawo tarihin kafuwar makarantar tun daga 1925, inda ya ce ta samo asali ne daga Makarantar Kofar Sauri.

Ya bayyana yadda makarantar ta sauya suna daga Provincial Secondary School a 1952, zuwa Government Secondary School Katsina a 1967, Government College a 1978, Government Pilot Secondary School Katsina a 2000, kafin daga bisani gwamnatin jihar ta amince da sauya sunanta zuwa Kwalejin Dikko.

Ya jero manyan nasarorin da ƙungiyar ta cimma, ciki har da sauya sunan makarantar, kafa sakatariyar ƙasa, sake gina gine-ginen da aka rushe, katangar makaranta, da kuma samar da ayyukan tallafi kamar na Babban Bankin Najeriya (CBN), ofishin Civil Defence da tashar kashe gobara da wasu fitattun tsoffin ɗalibai suka gina.

Ya kuma yabawa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Abdulmumini Kabir Usman, CFR, wanda shi ne Babban Mai Kula (Grand Patron) na Kwalejin, bisa goyon bayan kuɗi da na shawarwari da ya bayar, wanda ya ce sun taimaka matuƙa wajen cimma nasarorin da aka ambata.

A wajen laccar musamman ta bikin shekaru 100, Dr. Ibrahim Ida, Wazirin Katsina kuma tsohon ɗalibi (1963–1967), ya yi waiwaye kan rayuwarsa a makarantar, yana mai bayyana bikin a matsayin “zinariya” ta shekaru ɗari na manufa, ci gaba da alfahari.

Ya ce makarantar ta taka muhimmiyar rawa wajen gina ɗabi’a, shugabanci da ɗorewar zumunci a tsakanin tsoffin ɗalibai, yana mai bayyana Kwalejin Dikko a matsayin “tsohuwar makaranta mai daraja” da ta cancanci girmamawa.

A jawabinsa, Sarkin Katsina ya jaddada muhimmancin zumunci da haɗin kai, tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen gyara makarantar da ɗaga darajarta. Ya ce ya taba yin irin wannan kira a zamanin marigayi Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, amma ba a cimma nasarar aiwatar da shi ba.

A yayin bikin, an karrama fitattun alkalai da manyan mutane da lambobin yabo na girmamawa, ciki har da tsohon Alkalin Kotun Koli Justice Umar Walin Hausa, Dr. Umar Mutallab, Sanata Ibrahim Ida, tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Alhaji Mahe Rashid, da kuma sarakunan gargajiya da tsoffin gwamnonin tsohuwar Jihar Kaduna da Jihar Katsina.

Bikin ya kammala da kiran hadin gwiwa ga gwamnati, tsoffin ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki da su kare Kwalejin Dikko a matsayin gadon tarihi, abin alfahari da muhimmin ginshiƙi a tafiyar ci gaban ilimi da shugabanci a Jihar Katsina.

Follow Us