Rahotanni na Nuna Gwamnan Kano Na Dab da Sauya Sheka zuwa APC

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28122025_190830_IMG_0044.jpeg

Katsina Times 

Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kammala shirye-shiryen sauya sheka daga jam’iyyarsa zuwa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Majiyoyi sun nuna cewa gwamnan na shirin sanar da matsayinsa a kowane lokaci, bayan kammala tattaunawa da wasu muhimman abokan siyasar sa na kusa.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa cikin ‘yan watannin da suka gabata, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ƙoƙarin matsa wa ubangidan siyasar sa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya mara masa baya wajen komawa APC. Sai dai rahotanni sun ce tsohon gwamnan ya ƙi amincewa da hakan, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da zama a Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP).

Duk da maimaita yunƙurin shawo kan Kwankwaso, gwamnan bai samu goyon bayan sa ba kan batun sauya shekar ba.

Wata majiya daga Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana cewa gwamnan ya gana da wasu ‘yan majalisar tare da sanar da su shirin da yake yi. Majiyar ta ce ana sa ran Kakakin Majalisar zai fitar da sanarwa da ke tabbatar wa gwamnan cikakken goyon baya, komai irin matakin siyasar da zai ɗauka dangane da jihar.

Majiyar ta ƙara da cewa magoya bayan Sanata Kwankwaso su ma na shirin fitar da wata sanarwa ta daban, inda za su sake jaddada biyayyarsu ga jagoransu da kuma jam’iyyar NNPP.

“Za a ga yadda abubuwa za su fara bayyana cikin mako mai zuwa, domin gwamnan ya riga ya yanke shawara, duk da adawar Kwankwaso,” in ji majiyar.

A baya dai an yi jita-jitar cewa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin sauya sheka zuwa APC, zargin da Kwankwaso ya fito fili ya musanta. Kalaman suka da Sanatan ya dinga yi wa APC a baya-bayan nan sun ƙara tabbatar da ra’ayin masu lura da harkokin siyasa cewa ba ya da niyyar komawa jam’iyyar mai mulki.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin Gwamna Abba Kabir Yusuf da na Sanata Kwankwaso ya ci tura, domin ba su amsa kiran waya ko saƙonnin kar-ta-kwana da aka aike musu ba zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Follow Us