Daga Wakilanmu
@Katsina Times
Jaridar Katsina Times ta samu jerin ƙorafe-ƙorafe daga wasu mutane da kuma hukumomi, waɗanda ke iƙirarin sun kai muhimman takardu zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, amma takardun suka ɓace ba tare da an gano inda suka dosa ba, ko dai kafin su kai gaban Gwamna, ko kuma bayan Gwamnan ya sanya musu hannu.
Binciken da Katsina Times ta gudanar ya nuna cewa wannan shi ne karo na farko a tarihin Jihar Katsina da ake samun irin wannan ƙorafi mai yawa dangane da ɓacewar takardu a Gidan Gwamnati.
An bayyana cewa ko a zamanin mulkin tsohon Gwamnan jihar, Alhaji Aminu Bello Masari, CFR, wanda a wancan lokaci takardu ke shiga Gidan Gwamnati kai tsaye ba tare da tsaiko ba, ba a taɓa samun irin wannan koke ba.
Jaridar Katsina Times ta samu kwafen wasu daga cikin takardun ƙorafin, inda ta bi hanyoyi daban-daban na bincike.
Binciken ya tabbatar da cewa takardun sun shiga Gidan Gwamnati yadda ya kamata, amma suka “yi layar zana” a wani mataki ba tare da an san inda suka tsaya ba.
Haka kuma, jaridar ta samu irin waɗannan ƙorafe-ƙorafen daga wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati, waɗanda ke aikawa da takardunsu daga ofisoshinsu zuwa Gidan Gwamnati.
Sun bayyana cewa bayan aika takardun, sukan shafe lokaci suna jira ba tare da samun wata amsa ba. Sannan idan aka yi bincike sai a rasa wace hanya takardar ta bi, balle a gano inda take.
Dukkan masu ƙorafin, ciki har da ma’aikatan gwamnati da kuma ɗaiɗaikun mutane, sun nemi a sakaya sunayensu bisa dalilan tsaro da kuma tsoron fuskantar bita da ƙulli.
Duk da haka, sun gabatar wa Katsina Times da hujjoji masu ƙarfi waɗanda ke da wahalar yin watsi da su.
Lamarin ya fara zama ruwan dare, har ma ana jin wasu masu bin takardu suna furta kalaman kamar: “Allah ya sanya a ganta”, furuci da ba a saba ji ba a baya a irin wannan al’amari.
Sai dai binciken Katsina Times ya tabbatar da cewa Gwamnan Jihar Katsina bai taɓa yarda wata takarda ta kwana sama da awa 48 a kan teburinsa ba tare da ya sanya mata hannu ko ya fitar da ita ba.
An ruwaito cewa Gwamnan ya taɓa faɗa wa wasu da suka tunatar da shi game da wata takarda cewa: “Ba wata takarda a ofishina. Duk na fitar da su.”
Binciken ya kuma nuna cewa Gwamnan na tsayawa tsayin daka wajen gudanar da aikinsa, inda idan yana ofis ba ya karɓar baƙi sai waɗanda ya gayyata, kuma ba a shiga ofishinsa kai tsaye (gandasa).
Wannan ya ƙara tabbatar da cewa ba a barin takardu su yi jinkiri a teburinsa.
Jaridar Katsina Times ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulƙadir Mamman Nasir (Andaje), domin gano inda matsalar take. Sai dai duk da ƙoƙarin da aka yi tsawon kwanaki 10, ta hanyar kira da saƙonnin waya, ba a samu damar jin ta bakinsa ba.
A ƙarshe, masu ƙorafin na fatan Allah Ya sanya shekarar 2026 ta zama shekarar da za a yi wa takardun jama’a adalci a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, domin tabbatar da gaskiya, amana da ingantaccen aiki a harkokin gwamnati.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Facebook; katsina city news
Alll social media handles. Katsina times
07043777779