Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
A ranar farko ta sabuwar shekarar 2026, al’ummar Karamar Hukumar Dandume sun wayi gari da wata takarda da ake dangantawa da Katsina State Community Watch Corps, wadda ke umartar direbobin mashina da masu sana’ar sufuri da bin wasu ƙa’idoji, tare da barazanar hukunci mai tsanani da zaman gidan yari ga duk wanda ya karya doka.
Sai dai, abin takaici, wannan takarda ta haifar da tambayoyi masu yawa fiye da amsoshi.
Da fari, takardar tana ɗauke da kwanan wata 02 ga Janairu, 2026, alhali kuma an fara yada ta ne a ranar 01 ga Janairu, 2026, ranar farko ta sabuwar shekara. Wannan kuskure ya isa ya bayyana kin amincewa da sahihancin takardar, tare da nuna gaggawa da rashin bin ka’idojin aiki a hukumance.
Abu na biyu, kuma mafi muhimmanci, shi ne ketare iyaka ta fuskar doka. A bayyane yake cewa kula da ababen hawa, tantance su, da hukunta masu laifin zirga-zirga, hakki ne da doka ta bai wa Hukumar KASSAROTA, ba Katsina State Community Watch Corps ba. An kafa Community Watch ne domin tallafa wa tsaron al'umma, (Musamman Matsalolin masu garkuwa da mutane), ba domin tsayar da ababen hawa ko tsoratar da jama’a da hukuncin gidan yari ba.
Wani abin damuwa kuma shi ne yadda takardar ta yi barazanar hukunci mai tsanani da zaman gidan yari, ba tare da ambaton ko da sashi ɗaya na dokar Jihar Katsina ko ta ƙasa da ta ba da wannan iko ba. A kowace kasa mai bin doka, hukunci ba ya wanzuwa sai an jingina shi da takamaiman doka. Duk wata barazana da ba ta da tushen doka, barazana ce ga ‘yancin dan Adam.
Abin da ya kara da shakku a lamarin shi ne cewa takardar ta fito babu sa hannu, babu suna, babu mukami, kuma babu hatimin hukuma. Wannan ya saba wa ka’idar sanarwar gwamnati, kuma ya bar al’umma cikin ruɗani: shin wannan sanarwa ta hukuma ce, ko kuma aikin wasu mutane ne da ke kwaikwayon hukuma?
Salon rubutun takardar ma ya nuna rashin ƙwarewa da horo, abin da ke iya nuni da raina hankalin jama’ar Dandume. A zamanin da ake kira dimokuradiyya da bin doka da oda, bai kamata wata hukuma ta rika mu’amala da jama’a cikin ruɗani da tsoratarwa ba.
Idan har wannan takarda da gaske ta fito daga Katsina State Community Watch Corps, to lallai akwai buƙatar gyaran tsari cikin gaggawa, horar da jami’ai, da fayyace iyakokin aiki tsakanin hukumomi. Amma idan ba daga hukuma ta fito ba, to wajibi ne hukumar ta fito ta bayyana gaskiya tare da ɗaukar matakin da ya dace.
A ƙarshe, al’ummar Dandume ba su cancanci a rika gwada dokoki a kansu ba. Abin da suke bukata shi ne tsaro, adalci, da mutunta su a matsayin ‘yan kasa masu haƙƙi, ba tsoratarwa ba.