Gasar Dan’amana Cup Ta Kafa Sabon Tarihi Ga Kwallon Kafa a jihar Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05012026_185107_FB_IMG_1767639001757.jpg

Katsina Times 

An bayyana gasar kwallon kafa ta Dan’amana Cup a matsayin wani gagarumin tarihi a fannin ci gaban wasannin matasa a Jihar Katsina, bayan kammala gasar cikin nasara a ranar Lahadi, 4 ga Janairu, 2026.

Da yake zantawa da Katsina Times, Shugaban Kwamitin Shirya Gasar (LOC), Malam Ayuba Umar Gambarawa, ya ce gasar ita ce ta farko irinta a jihar, duba da girma da tasirin da ta yi, inda ya jaddada cewa ta bar babban tarihi a bangaren hadin kan al’umma da bunkasar matasa.

Gasar ta kunshi kungiyoyi 64 daga sassa daban-daban na Jihar Katsina, kuma ta samu kulawa ta musamman daga kafafen yada labarai da jama’a tun daga fara wasanni har zuwa wasan karshe tsakanin Gawo Professional da Durbi Strikers. A cewarsa, dukkan kungiyoyin da suka shiga gasar sun amfana tun kafin fara wasannin, sannan bayan kammala gasar ma an kara basu tallafi.

Malam Ayuba Gambarawa ya bayyana cewa kungiyoyin da ba su kai zagaye na goma sha shida ba an sake basu kwallaye, yayin da kungiyoyi 16 da suka tsallaka matakin sun samu riguna masu inganci. Haka kuma, kungiyoyin da suka zo na daya zuwa na hudu sun samu kyaututtuka na musamman, abin da ya ce bai taba faruwa ba a tarihin kwallon kafa ta jihar Katsina.

Gasar ta samu daukar nauyi ne daga Dan’amana na Katsina, Dakta Haruna Umar Maiwada, wanda a cewar shugaban LOC, ya dauki nauyin gasar gaba daya da kudinsa domin bunkasa wasannin matasa da karfafa ci gaban jihar.

Rahotanni sun nuna cewa gasar ta taka muhimmiyar rawa wajen hada kan matasa da kuma kara karfafa goyon bayan jama’a ga gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umar Radda, PhD, musamman a lokacin wasan karshe da ya samu halartar jama’a da dama.

Malam Ayuba Gambarawa ya yaba da yadda aka gudanar da gasar cikin tsari da lumana, yana mai cewa duk da wasu kalubale kadan, nasarorin da aka samu sun fi karfi. Ya bukaci sauran masu ruwa da tsaki da ’yan siyasa su yi koyi da irin wannan shiri da ke amfani kai tsaye ga matasa.

Ya taya kungiyoyin da suka yi nasara murna, tare da karfafa gwiwar wadanda ba su samu damar zuwa gaba ba, yana mai cewa kwallon kafa, kamar rayuwa, na kunshe da nasara da kuma rashin nasara.

Ana kallon gasar Dan’amana Cup a matsayin abin koyi ga shirye-shiryen wasanni na matasa a nan gaba a Jihar Katsina.

Follow Us