Kungiyar Kanikawa ta Jihar Katsina (NATA) ta kai ziyarar dubiya ga makarantar koyar da Kanikanci ta zamani da Hukumar Tallafawa Manyan Makarantu ta Gwamnatin Tarayya (TETFUN) ke ginawa.
Shugaban NATA na jihar, Injiniya Abbati Muhammad Unguwar Alkali, a yayin jawabinsa bayan kammala ziyarar, ya bayyana cewar aikin gina makarantar ya samo asali ne daga tsohon Gwamnan Jihar Katsina kuma shugaban TETFUN, Hon. Aminu Bello Masari, domin bunkasa koyarwar Kanikanci da zamanantar da shi.
“Wannan aikin, mafi girma sakon da yake isarwa shi ne rage zaman banza da talauci a cikin al’umma,” in ji Injiniya Abbati.
Ya kara da cewa za a gina makarantar ne a Katsina domin amfanar da matasa daga dukkanin fadin jihar, yana mai cewar har ma da wadanda ba su halarci makarantar boko ba za su ci moriyarta. Abbati, ya kuma yaba wa gwamnatin jihar ta hannun Malam Dikko Umar Radda bisa goyon bayan da take bai wa aikin.
Injiniya Abbati ya sha alwashin cewar NATA za ta ci gaba da ziyarar dubiya lokaci-lokaci har aikin ya kammala, domin tabbatar da inganci da bayar da gudummawar da ya dace daga kungiyar.
Injiniya Umar Jariri, wanda ke jagorantar aikin ginin, ya jinjinawa NATA bisa gudummawar da suke bayarwa wajen rage zaman banza da samar da ayyukan yi ga matasa. Haka zalika, ya yaba wa gwamnatin jihar da TETFUN bisa kafa cibiyar koyar da Kanikanci a Kwalejin Hassan Usman Katsina, wadda za ta samar da matasa masu kwarewa iri-iri.
A yayin ziyarar dubiyar dai, shugabannin NATA da membobinsu sun zagaya inda suka duba Bangarorin gudanarwa, Zaure na aikace-aikacen Kanikanci, Dakunan darussan aikin hannu, Wajen kwanan dalibai, Dakin taro, Dakin girki, da sauran sassa.
Makarantar, kamar yadda injiniyoyin suka bayyana, za ta kasance cibiyar koyar da Kanikanci ta zamani wacce za ta kawo ci gaba ga jihar Katsina da ma sauran jihohi makwabtanta. Hakazalika, za ta bai wa matasa damar koyon sana’o’i daban-daban da inganta rayuwarsu.