Daga Mu’azu Hassan
@Katsina Times
Jaridar Katsina Times ta tattauna da mutanen garin Jiƙamshi da ke ƙaramar hukumar Musawa a jihar Katsina kan yadda ɓarayin daji suka kai musu hari a yammacin ranar Talata, 10 ga watan Maris.
ASALIN LAMARIN
A ranar Litinin, 9 ga watan Maris, wasu Fulani sun kawo shanu a kasuwar Jiƙamshi domin su sayar. Sai dai wasu sojoji suka biyo shanun suka ƙwace su, kamar yadda wasu mutanen da abin ya faru a gabansu suka tabbatar wa jaridar.
Majiyoyin sun ce Fulani masu shanun ba su yi wata turjiya ba, sun janye jikinsu ne suka bar sojojin suka tafi da shanun.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ƙananan hukumomi a Jihar Katsina na da wata yarjejeniya da Fulani masu ɗauke da makamai, inda za su daina kai hare-hare, su kuma a ƙyale su su riƙa zuwa kasuwanni domin yin ciniki. Ƙaramar Hukumar Musawa na cikin waɗanda ake cewa suna da irin wannan yarjejeniya.
YADDA AKA KAI HARIN
A ranar Talata da misalin ƙarfe 6 na yamma, ɓarayin sun iso garin Jiƙamshi ta hanyar garin Kogari, a kan mashina masu yawa.
Sun raba kansu gida uku tare da riƙa banka wa shaguna da gidaje wuta a wurare daban-daban.
Ɓarayin sun riƙa bin shaguna da gidaje suna kwasar kayayyaki tare da amsar wayoyin mutane.
Wani mutum da abin ya rutsa da shi a shagonsa ya shaida wa jaridar Katsina Times cewa: "Da suka ɓalle shagunan suka gan mu a ciki, sai muka ɗaga hannu muka yi saranda. Amma sai suka bubbuge mu suka ce mu gudu.”
Majiyoyi sun kuma tabbatar wa jaridar cewa duk wanda ya gudu ko ya yi saranda, ɓarayin ba su kashe shi ba.
Mutanen garin sun ce ɓarayin sun yi ta'addacinsu a cikin garin na kusan awa ɗaya da rabi, sannan suka taru a wuri guda suka bi hanyar da suka shigo, wato hanyar garin Kogari, suka fice.
ZUWAN JAMI’AN TSARO
Mutanen garin sun ce jami’an tsaro sun iso garin ne bayan ɓarayin sun tafi. Sun ce sun nuna musu hanyar da ɓarayin suka bi, amma ba su yi wani yunƙurin bin su ba.
Jami’an tsaron sun tsaya a garin har zuwa wayewar garin ranar Laraba.
AN YI JANA’IZAR MUTANE 3
Da safiyar ranar Laraba, jama’ar garin sun fita domin duba irin ɓarnar da aka yi, wadda ta haɗa da fasa shaguna da gidaje.
Sun kuma tabbatar da cewa ɓarayin sun kashe mutane uku a yayin harin.
Mutanen garin sun ce ɓarayin ba su tafi da kowa ba. Wata mata da aka yi zaton sun tafi da ita saboda dukan da suka yi mata, daga baya an gan ta ta dawo.
A cewar mutanen garin, suna zargin cewa ɓarayin sun zo ne domin ɗaukar fansar abin da suka ce sojoji sun yi musu na ƙwace shanunsu.
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, babu wata sanarwa daga jami’an tsaro ko Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Jihar Katsina dangane da harin da aka kai garin Jiƙamshi.
Katsina times
Www.katsinatimes.com
Facebook page: katsina city news
Social media handles. Katsina times