Daga Wakilanmu @ Katsina Times
An gurfanar da Aminu Nasta a wata kotu da ke Abuja bisa zargin lalata wani allo mai ɗauke da hoton Shugaban Ƙasa, da kuma balle wani ofishin jam’iyyar APC tare da yin awon gaba da kuɗaɗen da aka ajiye a ofishin, waɗanda yawansu ya kai Naira miliyan 35.
A cewar rahoton jaridar Sahara Reporters, Aminu Nasta ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa, ciki har da zargin cin amanar ƙasa da kuma sata.
Nasta ya bayyana cewa shi ne shugaban wata ƙungiya da ke kare martabar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamna Dikko Umar Radda, yana mai tambayar dalilin da zai sa ya aikata irin waɗannan laifuka.
Lauyoyin Nasta sun kalubalanci tuhumomin da aka gabatar a kansa tare da neman kotu ta bayar da belinsa.
Sai dai, lauyoyin masu gabatar da ƙara sun nemi kotun ta ba su ƙarin lokaci domin su ci gaba da tsare Nasta na tsawon makonni biyu, domin kammala binciken da suke gudanarwa.
Har zuwa lokacin da aka ɗage zaman kotun a ranar Talatar da ta gabata, kotun da ke Jiwa, a Babban Birnin Tarayya Abuja, ba ta bayar da belin Aminu Nasta ba.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page.katsina city news
Facebook .jaridar Taskar labarai
All social media handles @ katsina times
07043777779.


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!