"Ba Mu Tsoron Kowa, Kuma Wallahi Duk Wanda Ya Nuna Ma Dikko Hannu, To Sai Mun Nuna Ma Shi."

Inji Alhaji Samir Ismail (Wazirin Gwamna Radda).Alhaji Samir Ismail Musawa, (Wazirin Gwamna Radda) ya bayyana cewa, basu taron kowa kuma duk wanda ya nuna ma gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko…

Katsina City News September 09, 2026  ·  12:00 AM
| 24 Views
"Ba Mu Tsoron Kowa, Kuma Wallahi Duk Wanda Ya Nuna Ma Dikko Hannu, To Sai Mun Nuna Ma Shi."
"Ba Mu Tsoron Kowa, Kuma Wallahi Duk Wanda Ya Nuna Ma Dikko Hannu, To Sai Mun Nuna Ma Shi."


Inji Alhaji Samir Ismail (Wazirin Gwamna Radda).


Alhaji Samir Ismail Musawa, (Wazirin Gwamna Radda) ya bayyana cewa, basu taron kowa kuma duk wanda ya nuna ma gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda hannu to a shirye suke suma su nuna ma shi, ya bayyana hakan ne a ranar Talata 08/9/2026, wajen kaddamar da tsare-tsaren ƙungiyar Dikko Radda Awareness Movement.


Ya fara da cewa "Mun assasa wannan ƙungiyar ne akan abubuwa guda uku, na farko mun kafa ta ne bisa akida da kishi, da taimakon juna, da taimakon al'ummar mu, na biyu kuma mun kafa ta ne saboda jam'iyar mu ta APC saboda cikin ta muke iya zama komi, na uku, mun kafa ta ne saboda kishin jagoranmu wanda shi ne uban tafiya, Malam Dikko Umar Radda.


Ya cigaba da cewa "Ina kira ga dukkanin matasan jihar Katsina da Mata da Maza yana da kyau mu samar da irin waɗannan ƙungiyoyin mu kafa ma kanmu, idan ka kalli kasashen da suka cigaba, zaka ga al'ummar ta, ta canza mulki ba mulki ya canza al'umma ba, to mu zama al'umma da ke iya canza tsarin, ba tsarin ya dinga juya mu yana canza mu ba. Inji shi.

Advertisement

NRS Gateway


Har wala yau, Wazirin Gwamna Radda ya cigaba da cewa "Jihar Katsina jiha ce ta musulunci kuma ta musulmai da Kiristoci, bamu da maguzawa da yawa, to da Musulmi da Kirista dukkanin mu muna da littafi daga ubangijin mu, ba zamu sha wahalar zama da junan mu ba, ina kiran matasa ba wai dan ina makusanci ga gwamna Radda ba, ina kiran matasa indai cigaban jihar Katsina kake nema, to duk sadda zaka bi shugaba to ka kalli wa zaka bi.


Wadannan gwamnatin ta Katsina, jam'iyyar APC ta gwamna Dikko Umar Radda ce, ko ka zauna ciki ko ka fita, kuma ko daga ina kake, kuma ko da wa kake takama, a jihar Katsina jami'yar APC ta Dikko Umaru Radda ce, ba ka iya kafa ta ka, sai dai ka bi Malam Dikko, ko kuma duk wani abu da kake so kayi to ba zaka samu nasarar shi ba, sannan kuma sai Dikko ya zama jagora ko kana so ko baka so,


Ba zai taba cin alfarmar wani ba sai dai kaci alfarmar shi, kuma ba'a zaben Dikko dan kai, sai dai a zabe ka dan shi, ba wanda ya isa daga wani gari, ko daga wata kujera ta Federal, shi Dikko aiki yake yi, kuma zamu yi Asuwaju da Dikko, saboda gwamnatin Najeriya ta gwamna ce da shugaban kasa, ko waye kai sai anci sannan za'a yi maka alfarma, kujerar alfarma ce karya kake ba zaɓar ka aka yi ba.


Daga karshe ya yi kira ga mambobin ƙungiyar da su bayar da gudummawa wajen taimakon Malam Dikko Umar Radda, da kuma jihar Katsina, tare da samar da nagartattun mutane daga cikin ta wadanda zasu jagoranci al'umma, watan wata rana, tare da kaucewa ma dukkanin ayyukan da zasu jawo ma matasa nakasu ko rushewar cikar burin su.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 4 + 3?