ADC ta gabatar da Addu'ar ci gaban Najeriya da neman agaji daga Allah a Katsina

A yau (Asabar 19/9/2027) ne jam'iyyar ADC, reshen jihar Katsina ta kira malamai mahaddata Al'Qurani mai girma a inda su ka sauke littafin mai tsarki da girma bayan fara karatu…

Katsina City News September 19, 2026  ·  12:00 AM
| 29 Views
ADC ta gabatar da Addu'ar ci gaban Najeriya da neman agaji daga Allah a Katsina
ADC ta gabatar da Addu'ar ci gaban Najeriya da neman agaji daga Allah a Katsina


A yau (Asabar 19/9/2027) ne jam'iyyar ADC, reshen jihar Katsina ta kira malamai mahaddata Al'Qurani mai girma a inda su ka sauke littafin mai tsarki da girma bayan fara karatu tun da sanyin safiya har zuwa la'asar wanda daga bisani kuma wasu da ga cikin manyan malamai da sauran al'ummomi aka hadu aka gabatar da sallar la'asar sannan malaman suka jagoranci addu'o'i.


Addu'o'in sun hada da rokon Allah Subhaanahu Wa Ta'ala Ya kara sa hannu a al'amurran Najeriya, musamman wadanda suka addabi kasar mu wadanda suka hada da harkar tsaro, ta'addanci, talauci, yunwa, dambarwar siyasa da cututtuka. 


A lokacin da yake jawabin maraba, shugaban wadanda suka hada taron, Honourable Abdurrazak Kaita na kungiyar gangamin 'yan takarar majalisar wakillai na jihar Katsina, ya ce bukatar taron ya zo ne domin munanan kuncin rayuwa na rashin tsaro, talauci da gurbacewar 'yan siyasa wanda wadanda ke rike da madafan iko su ka sa al'ummar Najeriya a ciki.


Haka shi ma a lokacin da yake jawabi, mai magana da yawun dan takarar gwamnan jihar Katsina, Abubakar Ahmed ya yi godiya kwarai da irin tunanin da wadanda suka shirya taron suka yi da fatan Allah Ya amsa.


Haka kuma a taron wanda ya sami halartar daruruwan mutane kuma ya gudana a ofishin dan takarar gwamnan jihar Katsina karkashin jam'iyyar ADC, Sanata Ahmad Babba Kaita, an roki Allah da Ya kawo mana saukin rayuwa da ci gaba, arziki da wadata da zaman lafiya a birane da kauyukan mu.


Addu'o'in ba su bar masu taimaka ma 'yan ta'addan ba a birane da kauyuka na kasar mu, a inda aka roki Allah da Ya tona asirin su, Ya tozarta su Ya kuma kawo karshen dukkan ta'addanci, cuta, cin hanci da rashawa da kuma sama da fadi da dukiya da hakkokin al'umma. 

Advertisement

NRS Gateway


Mahalarta taron sun kuma yi amfani da damar sun roki Allah Ya kara ma dan takarar gwamnan jihar ta Katsina, Sanata Ahmad Babba Kaita lafiya a yayin da ya ke kara samun saukin jinyar da ya yi, sannan an yi ma shi fatan Allah Ya dawo da shi lafiya da nasara a zaben da ke tafe. 


Haka zalika an roki Allah Ya ba dukkan 'yan takarkarin jam'iyyar ADC nasara da rikon amana da kawo sauyin da zai kawo karshen dukkan damuwa a Najeriya. 


Taron ya sami halartar malamai da yawa da mata da shugabanni har da wadanda ba na jam'iyyar ADC ba.


Sa hannu 

Abubakar Ahmed 

Jami'in hudda da jama'a na Kanfen Sanata Ahmad Babba Kaita 

19/9/2026

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 4?