Ni na ajiye mukamin don kashin kaina, ban fitar da wasiƙar ba don girmama gwamnan Katsina – Inji Abba Zayyana, tsohon shugaban KTTV

Daga Mu’azu Hassan@ Katsina TimesTsohon shugaban gidan talabijin na KTTV, Alhaji Abba Zayyana, ya bayyana wa jaridun Katsina Times cewa ba a sauke shi daga mukaminsa ba, shi da kansa…

Katsina City News November 10, 2026  ·  12:00 AM
| 188 Views
Ni na ajiye mukamin don kashin kaina, ban fitar da wasiƙar ba don girmama gwamnan Katsina – Inji Abba Zayyana, tsohon shugaban KTTV
Ni na ajiye mukamin don kashin kaina, ban fitar da wasiƙar ba don girmama gwamnan Katsina – Inji Abba Zayyana, tsohon shugaban KTTV


Daga Mu’azu Hassan

@ Katsina Times

Tsohon shugaban gidan talabijin na KTTV, Alhaji Abba Zayyana, ya bayyana wa jaridun Katsina Times cewa ba a sauke shi daga mukaminsa ba, shi da kansa ya ajiye mukamin bisa radin kansa tun ranar 2 ga watan Nuwamba.

Ya ce an ba shi shawarar ya fito fili ya sanar da ajiye mukamin, amma ya ƙi yin hakan saboda yana ganin hakan zai zama rashin girmamawa ga gwamnan da ya ba shi damar yin aiki a ƙarƙashinsa.

Ya ce, kowa yana da irin tsarin rayuwarsa da kuma tarbiyyar da ya samu daga gida.

"Ni, a yadda aka koya mini, ba zan watsa wa shugabana ƙasa a fuska ba. Wannan ne ya sa cikin girmamawa na ajiye mukamin, kuma na bar maganar a matsayin ta aiki kawai."

Zayyana ya ce babu wani laifi da aka yi masa, kawai ya nemi wa kansa mafita ne ta yadda zai samu damar gina rayuwarsa.

Advertisement

NRS Gateway

Katsina Times ta tuntube shi kan ko yana da wata alaƙa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Kabir Ibrahim Masari.

Zayyana ya ce, "Masari shugabana ne, kuma uba ne. Dakta Muttaqa Rabe wanane, ne, kuma ɗan uwana. Alhaji Jabiru Tsauri kuwa aminina ne. Wannan ita ce dangantakarmu."

Binciken Katsina Times ya gano cewa bayan fitar da sanarwar cire Zayyana daga shugabancin KTTV, da kuma wasiƙar da ya fitar wadda ya bayyana cewa shi da kansa ya ajiye mukamin, jama'a sun fi gamsuwa da wasiƙarsa fiye da sanarwar da aka fitar.

Binciken Katsina Times ya kuma gano cewa mutane da dama da suka san gwamnan sun bayyana cewa tun bayan hawansa mulki bai taɓa korar kowa daga aikinsa ba. Don haka, a wannan karon, mai yiwuwa akwai wani abu da ya faru, ko kuma an ba shi shawara marar kyau.

Katsina times 

@ www.katsinatimes.com 

Facebook page; katsina city news 

Facebook page.jaridar Taskar labarai

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 1?