An kammala dukkan karɓar bakuncin Babban Taron Inganta Rayuwar Matasa Da Samar Ma Su Damarmaki Watau 'Youth Opportunity Summit' na 2025, a jihar Katsina.
Wannan dai wani muhimmin taro ne da zai mayar da hankali wurin ƙarfafa gwuiwa matasa maza da mata a faɗin Najeriya. Taron na bana mai taken “Amfani da Dama: Gina Matasan Da Suka Shirya Tunkarar Ƙalubalen Da Ke Gaba” zai gudana daga ranar 9 zuwa 10 ga Mayu, 2025, a Babban Ɗakin Taro (Auditorium) na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.
Wannan taron dai wanda ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ke ta shirya kuma Babbar Mai Ba Shi Shawara kan Harkokin Mata da Matasa, Hajiya Hauwa Liman, ke jagorantar aiwatar da shi ya yi daidai da ƙudurin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaban matasa.
Haka zalika an tsara taron ne domin zaburar da matasa da mata, haɗa kan su, da kuma samar ma su da damar shiga a dama da su samun dama a harkokin cigaba a cikin gida da wajen Najeriya don ci gaban kansu da sana’o’insu, da kuma inganta tasirin da suke da shi a cikin al’ummominsu.
Taron zai samu halartar manyan baƙi da masana a fannoni daban daban ciki har da Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Shugaban Ƙasa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa; Sanata Ibrahim Ida, Wazirin Katsina, fitaccen ɗan siyasa kuma mai fafutukar ci gaban matasa; Farfesa Idris Bugaje, Babban Sakatare na Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Ƙasa (NBTE); da Mohammed Abu Ibrahim, Babban Sakatare na Asusun Raya Harkokin Noma na Najeriya (NADF).
Wasu ministocin tarayya daga ma’aikatun Ci Gaban Matasa, Ilimi, Al’adu, Tattalin Arziki na Ƙirƙira da Yawon Bude Ido, Sadarwa, Ƙirƙira da Tattalin Arziƙin Fasahar Zamani ma za su halarci taron.
Za a gabatar da maƙaloli, baje kolin kasuwanci a cikin yaren Hausa, baje kolin abubuwa daban-daban, kuma za'a ware wani bangare domin bayar da shawarwari ga ƴan kasuwa daga ƙwararru a fannoni daban daban duk a wannan taron na kwanaki biyu.
Babban manufar taron ita ce samar da hanyoyin da za su ƙara buɗe kofa da matasa domin su shiga cikin harkokin mulki, kasuwanci, da kuma sabbin fasahohi.
Ana sa ran sama da matasa da mata dubu ɗaya daga faɗin jihar Katsina da yankuna makwabta za su halarci wannan taro na kwanaki biyu, tare da goyon baya daga hukumomin gwamnati, ƙungiyoyi ma su zaman kan su da wadanda ba na gwamnati ba, da masu ruwa da tsaki daga kamfanoni masu zaman kansu.