KASSAROTA Ta Kaddamar da Horon Jaha Don Ƙarfafa Tsaro a Hanya da Inganta Aikin Jami’ai

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12052025_151250_FB_IMG_1747062593854.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

A wani sabon yunƙuri na inganta tsaro a hanya da kuma ƙwarewar aiki, Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA) ta fara wani cikakken shirin horaswa ga jami’an aiki da na ofis a faɗin dukkanin yankuna 13 na jihar.

Daraktan Hukumar kuma Shugaba na KASSAROTA, Manjo Garba Yahya Rimi (mai ritaya), ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin horon da aka gudanar a birnin Katsina. Ya bayyana cewa shirin wata dabarar gina ƙwarewar ma’aikata ce, domin inganta ƙwarewa da ɗawainiyar jami’an da ke taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da dokokin zirga-zirgar ababen hawa da kuma kare lafiyar mutane a tituna.

“Wannan horo wani ɓangare ne na ƙoƙarinmu na ƙara gogar da ayyukan jami’an KASSAROTA, daidai da hangen Nesa na Gwamna Dikko Umaru Radda na ganin hanyoyi sun zama masu aminci da inganci a faɗin jihar,” in ji Rimi.

Shirin horaswar ya biyo bayan umarnin gwamnatin jihar ne tun a shekarar 2023, wanda ya kai ga ɗaukar jami’ai 304. Ko da yake an bai wa jami’an horo na farko a Kwalejin Ƙasa ta Civil Defence, ba a sake basu wani horo ba tun daga lokacin. A cewar Rimi, hakan ne ya haifar da buƙatar sake sabunta musu ilimi da basu horo na ƙwarewa don su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Da amincewar Gwamna, ta hannun Kwamishinan Ayyuka, KASSAROTA ta zaɓi jami’ai biyu daga kowace cibiyar yankinta guda 13 — ɗaya na aiki kai tsaye a titi, ɗaya kuma na ofis. Wadannan yankuna sun haɗa da manyan cibiyoyin zirga-zirga kamar Katsina, Daura, Funtua, Malumfashi, Danja, Kankara, Dutsin-ma, Jibia, Mai’adua, Mashi, Kankia da sauransu.

Jami’an da ke aiki a titi su ne ke da alhakin lura da ayyuka na kullum a tituna, da sa ido kan ɗabi’ar jami’ai da tabbatar da bin doka. Na ofis kuwa, su ne ke gudanar da ayyukan rubuce-rubuce, kididdiga da bayar da rahotanni. Horon ya tanadi abubuwa daban-daban da suka shafi bukatun kowane ɓangare, tare da nufin ƙarfafa haɗin kai tsakanin jami’an filin aiki da na ofis.

Rimi ya ce jami’an da ake horarwa ana sa ran za su yada ilimin da suka samu ga abokan aikinsu a yankunansu, don samun sakamako mai faɗi a hukumance.

“Kara ilimi da fahimtar jami’anmu zai inganta aikinsu na yau da kullum, rage haɗurran hanya, daidaita zirga-zirga, da ƙara amincewar jama’a da ayyukanmu,” in ji shi.

Wannan shirin na nuna yadda KASSAROTA ke amfani da dabarar zuba jari ga ma’aikatanta domin fuskantar kalubalen tsaro a tituna. Jami’ai sun bayyana cewa horon wata hanya ce ta sauya fasalin hukumar domin gina ingantacciyar hukuma mai kula da zirga-zirgar ababen hawa, wadda za ta dace da bukatun hanyoyin birane da ƙauyuka masu kara yawaita a jihar Katsina.

Follow Us