Nazarin Jaridun Katsina Times
Siyasar 2025 zuwa 2027 ta shiga wani sabon shafin karatu wanda ba a saba ganin shi a kundin ilmin dimokaradiyya ta Nijeriya.
'Yan adawa na zargin ana amfani da barazana da ƙarfin gwamnati ana firgita duk wani wanda ake tsammanin zai iya fuffuka a zaɓen 2027.
'Yan adawa na zargin ana hana Manyan jam'iyyun adawa zaman lafiya balle har su sami damar da za su nemi yin wani tasiri a zaɓen 2027.
Misali har yanzu an rasa wane dalili mai ƙarfi yake sanya ka ga gwamnatin jiha baki ɗaya ta koma jam'iyya mai mulki? An fi zargin barazana.
Wane dalili ke sanya 'yan majalisun tarayya da sanatoci ke tururuwa?
Wani rahoton jaridar Daily Trust ya ce ana zargin ba da toshiyar baki ta hanyoyi daban-daban.
A Arewa maso Yamma har yanzu jama'a na koke da tashin gwauron zabi na farashin kaya, kuma har yanzu ba abun da aka yi a ƙasa na warware matsalar.
Har yanzu matsalar tsaro ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa a Arewa baki ɗayanta.
Ga zargin bambancin da gwamnatin tarayya ke nunawa tsakanin Kudu da Arewa, wanda ana zargin an ba 'yan Kudu muƙamai masu kauri, amma an ba 'yan Arewa muƙamai masu rawa.
Zaɓen 2027, zai zama tsakanin APC ne da talakawa. Ko da sun amshi taliya, za su nuna mata cewa ƙuri'arsu 'yancinsu.
A zaɓen 2027, ko dai talakawan ƙasar nan su nuna wa APC cewa duk mun ji zafin matakan da kuka ɗauka, ko su zama tumakai.
Zaɓen 2027 tsakanin APC ne da talakawa. Akwai yiyuwar wasu gwamnonin za su iya tsallakewa saboda kyakkyawar dangantakarsu da talakawa, akwai kuma waɗanda za a yi masu saki uku ba kome.
Akwai yiyuwar cin zaɓen fitar da gwani ko cusa wasu 'yan takara ba zai yi amfani ba ga wasu 'yan majalisun daga jiha har tarayya har zuwa sanatoci.
Wanda zai fi shan wahala a zaɓen 2027, shi ne wanda jam'iyyar APC ta tabbatar shi ne zai mata takara, musamman Bola Tinubu za a siyar da shi da wahalar gaske.
Allah ne kaɗai ya san me zai faru.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762