Katsina Times
Majalisar Masarautar Kano ta fitar da wata sanarwa mai dauke da umarnin cewa dukkan Hakimai da ’yan Majalisa su shigo cikin Birnin Kano tare da dawakan su domin gudanar da bikin Hawan Babbar Sallah.
Sanarwar, wacce Sakataren Majalisar Kano, Alhaji Abba Yusuf, ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa an tsara zuwan ne a ranar Laraba, 8 ga watan Dhul Hijjah, 1446H, wanda ya yi daidai da 4 ga Yuni, 2025.
Majalisar ta kara da cewa a ranar Alhamis, 9 ga Dhul Hijjah, wanda ya yi daidai da 5 ga Yuni, 2025, da misalin karfe 11:00 na safe, za a gudanar da taro a Fadar Mai Martaba Sarkin Kano. Taron zai hada da jawabi daga Majalisa ga dukkan Hakimai da kuma tattaunawa kan yadda za a gudanar da Hawan Sallah na bana.
Har ila yau, Majalisar ta ce ta sanar da Shugaban Karamar Hukumar Kano domin tabbatar da samun hadin kai da tsari a lokacin da mahalarta za su shigo birnin domin wannan muhimmin bikin.
Majalisar ta kammala sanarwar da fatan Allah Ya sanya a yi bikin lafiya da zaman lafiya a cikin Kano da daukacin kasa.